Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, “Ɗibi tokar matoya cike da tafin hannuwanku, Musa kuwa zai watsa tokar sama a gaban Fir’auna.

  2. Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, bai kuwa saurare Musa da Haruna ba kamar yadda Ubangiji ya riga ya ce wa Musa.

  3. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe, ka sadu da Fir’auna, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Ibraniyawa ya ce, Ka bar mutanena su tafi don su yi mini sujada,

  4. ko kuwa a wannan lokaci zan aika da cikakkiyar annoba mai ƙarfi a kanka da a kan fadawanka da mutanenka, domin ka san cewa ba kama da ni a dukan duniya.

  5. Gama da ni kaina na miƙa hannuna na buge ka da jama’arka da annoba, ai, da an hallaka ku a duniya ƙaƙaf.

  6. Amma na bar ka ka rayu domin in nuna maka ikona, domin kuma sunana yă zama abin darajantawa a dukan duniya.

  7. Har yanzu kana gāba da mutanena, ba ka kuma bar su su tafi ba.

  8. Saboda haka, gobe war haka, zan sa a yi ƙanƙara mai tsananin gaske, irin wadda Masar ba tă taɓa gani ba tun kahuwarta, har yă zuwa yanzu.

  9. Waɗansu daga cikin dattawan Fir’auna suka cika da tsoro saboda abin da Ubangiji ya faɗa, nan da nan suka shigo da dabbobinsu da bayinsu da sauri daga gona zuwa cikin gida.

  10. Amma waɗanda ba su kula da maganar Ubangiji ba, suka bar bayinsu da dabbobi a gona.

  11. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama don a yi ƙanƙara a bisa dukan Masar, a bisa mutane da dabbobi, da bisa dukan abubuwan da suke girma a gonakin Masar.”

  12. Da Musa ya miƙa sandansa sama, sai Ubangiji ya aiko da tsawa da ƙanƙara, da walƙiya har ƙasa. Ta haka Ubangiji ya yi ruwan ƙanƙara a bisa ƙasar Masar;

  13. Sai Fir’auna ya aika a kira Musa da Haruna. Ya ce musu, “A wannan karo na yi zunubi. Ubangiji, shi ne da gaskiya, ni da mutane mu ke da kuskure.

  14. Ku roƙi Ubangiji, yă tsai da tsawar da ƙanƙarar. Ni kuwa na yi alkawari zan bar ku ku tafi, ba za ku ƙara tsayawa a nan ba.”

  15. Musa ya amsa, “To, da kyau, da zarar na fita daga birnin, zan yi addu’a ga Ubangiji, tsawar za tă tsaya, ƙanƙarar kuma za tă daina, don ku sani cewa duniya ta Ubangiji ce.

  16. Amma na san cewa kai da fadawanka, har wa yau ba ku ji tsoron Ubangiji Allah ba tukuna.”

  17. Sai Musa ya tashi daga gaban Fir’auna, ya fita daga birni. Da ya miƙa hannuwansa ta wajen Ubangiji, sai tsawa da ƙanƙara suka tsaya, kwararowar ruwa kuma ta ɗauke.

  18. Ta haka zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa bar Isra’ilawa suka tafi ba, kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa ta wurin Musa.

  19. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je wurin Fir’auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da kuma zukatan fadawansa domin in aikata waɗannan mu’ujizai nawa a tsakiyarsu,

  20. don kuma ku gaya wa ’ya’yanku da jikokinku yadda na tsananta wa Masarawa, da kuma yadda na aikata mu’ujizai a cikinsu, don ku sani ni ne Ubangiji.”

  21. Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce masa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Ibraniyawa ya ce, ‘Har yaushe za ka ƙi ƙasƙantar da kanka a gabana? Ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada.

  22. In ka ƙi ka bari su tafi, gobe zan aiko da fāra a ƙasarka.

  23. Fadawan Fir’auna suka ce masa, “Har yaushe mutumin nan zai zama mana tarko? Ka bar mutanen su tafi domin su yi wa Ubangiji Allahnsu sujada. Har yanzu ba ka san cewa Masar ta lalace ba?”

  24. Sa’an nan aka dawo da Musa da Haruna wurin Fir’auna. Sai ya ce, “Ku tafi, ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada. Amma wa da wa za su tafi?”

  25. Musa ya amsa, “Za mu tafi tare da ƙanananmu, da tsofaffinmu, da ’ya’yanmu maza da mata, da kuma garkunanmu na shanu da tumaki, gama dole ne mu yi bikin ga Ubangiji.”