Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Idanunka irin na mutum ne? Kana gani yadda mutum yake gani ne?

  2. Kwanakinka kamar na mutane ne, ko shekarunka kamar na mutane ne

  3. da za ka neme ni da laifi ka hukunta ni?

  4. Ko da yake ka san ba ni da laifi, kuma ba wanda zai iya cetona daga hannunka.

  5. “Da hannuwanka ka ƙera ni, kai ka halicce ni. Yanzu kuma kai za ka juya ka hallaka ni?

  6. Ka tuna cewa ka mulmula ni kamar yumɓu. Yanzu za ka mai da ni in zama ƙura kuma?

  7. Ba kai ka zuba ni kamar madara ba, na daskare kamar cuku.

  8. Ka ba ni rai ka kuma yi mini alheri, kuma cikin tanadinka ka kula da ruhuna.

  9. “Amma wannan shi ne abin da ka ɓoye a zuciyarka, na kuma san abin da yake cikin zuciyarka ke nan.

  10. In na yi zunubi kana kallo na kuma ba za ka fasa ba ni horo ba don laifin da na yi.

  11. Idan ina da laifi, kaitona! Ko da ba ni da laifi, ba zan iya ɗaga fuskata ba, gama kunya ta ishe ni duk ɓacin rai ya ishe ni.

  12. In na ɗaga kaina, za ka neme ni kamar zaki ka sāke nuna al’ajabin ikonka a kaina.

  13. Kana sāke kawo sababbin waɗanda za su ba da shaida a kaina kana ƙara haushinka a kaina; kana ƙara kawo mini hari.

  14. “Me ya sa ka fito da ni daga cikin uwata? Da ma na mutu kafin a haife ni.

  15. Ka ce wa Allah, ‘Abin da na gaskata ba laifi ba ne kuma ni mai tsabta ne a gabanka.’

  16. Da ma Allah zai yi magana, yă buɗe baki yă faɗi wani abin da ka yi da ba daidai ba

  17. yă kuma buɗe maka asirin hikima, gama hikima ta gaskiya tana da gefe biyu. Ka san wannan, Allah ya riga ya manta da waɗansu zunubanka.

  18. “Ko za ka iya gane al’amuran Allah? Ko za ka iya gane girman asirin Maɗaukaki?

  19. “In ya zo ya kulle ka a kurkuku ya ce kai mai laifi ne, wa zai hana shi?

  20. Ba shakka yana iya gane mutanen da suke marasa gaskiya; kuma in ya ga abin da yake mugu, ba ya kula ne?

  21. “Duk da haka in ka miƙa masa zuciyarka, ka kuma miƙa hannuwanka gare shi,

  22. “Na zama abin dariya ga abokaina, ko da yake na yi kira ga Allah ya kuwa amsa mini, duk da haka suka yi mini riya ko da yake ni mai adalci ne kuma marar laifi!

  23. Amma wurin zaman ’yan fashi yana nan ba mai damunsu, waɗanda kuma suke saɓa wa Allah suna zamansu lafiya, har ma da masu ɗaukar allahnsu a hannuwansu.

  24. Wane ne cikin waɗannan bai san cewa hannun Ubangiji ne ya yi wannan ba?

  25. “Allah ne mai iko da kuma hikima, shawara da ganewa nasa ne.