Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Amma in za ka dubi Allah ka roƙi Maɗaukaki,

  2. in kai mai tsarki ne, kuma mai adalci, ko yanzu ma zai taimake ka, yă mayar maka iyalinka da farin cikinka.

  3. Abin da yake faruwa ke nan da duk wanda yake mantawa da Allah; waɗanda ba su da Allah, ba su da bege.

  4. “Ba shakka, Allah ba ya ƙin marar laifi, ko kuma yă ƙarfafa masu aikata mugunta.

  5. Sai dai yă cika bakinka da dariya, yă sa ka yi sowa ta murna.

  6. “Lalle, na san wannan gaskiya ne. Amma ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah?

  7. Ko da mutum yana so yă yi gardama da shi, ba zai taɓa amsa masa ba ko da sau ɗaya cikin dubu.

  8. Hikimarsa tana da zurfi, ikonsa yana da yawa. Wane ne ya taɓa yin faɗa da shi har ya yi nasara?

  9. Yana matsar da manyan duwatsu kafin su sani kuma yana juya su cikin fushinsa.

  10. Ba na iya ganinsa lokacin da ya wuce ni; ba na sani ya wuce lokacin da ya wuce.

  11. Wane ne ya isa yă hana shi in ya ƙwace abu? Wa zai ce masa, ‘Me kake yi?’

  12. Allah ba ya danne fushinsa; ko dodannin ruwan da ake kira ayarin Rahab ya tattake su.

  13. “Ta yaya zan iya yin faɗa da shi? Ina zan iya samun kalmomin da zan yi gardama da shi?

  14. Ko da na yi kira gare shi ya amsa mini, ban yarda cewa zai saurare ni ba.

  15. Zai sa hadari yă danne ni yă ƙara mini ciwona ba dalili.

  16. In maganar ƙarfi ne, shi babban mai ƙarfi ne! In kuma maganar shari’a ne, wa zai kai kararsa?

  17. Lokacin da bala’i ya kawo ga mutuwa, yakan yi dariyar baƙin cikin marasa laifi.

  18. Lokacin da ƙasa ta faɗa a hannun mugaye, yakan rufe idanun masu shari’a. In ba shi ba wa zai yi wannan?

  19. duk da haka ina tsoron duk wahalata, domin na san ba za ka ɗauke ni marar laifi ba.

  20. duk da haka za ka jefa ni cikin ƙazamin wuri, yadda ko rigunan jikina ma za su ƙi ni.

  21. “Shi ba mutum ba ne kamar ni wanda zan iya amsa masa, har da za mu yi faɗa da juna a wurin shari’a.

  22. wani wanda zai sa Allah yă daina duka na, don yă daina ba ni tsoro.

  23. Sa’an nan ne zan iya yin magana ba tare da jin tsoronsa ba, amma a yadda nake a yanzu ba zan iya ba.

  24. Zan ce wa Allah, kada ka hukunta ni, amma ka gaya mini laifin da na yi maka.

  25. Kana jin daɗin ba ni wahala, don me ka yashe ni, abin da ka halitta da hannunka, yayinda kake murmushi game da shirye-shiryen mugaye?