Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ya amsa ya ce, “Kina magana kamar wawiya. Alheri kaɗai za mu dinga samu daga Allah ban da wahala?” A cikin wannan duka Ayuba bai yi zunubi ba cikin maganarsa.

  2. Bari ranan nan ta zama duhu; kada Allah yă kula da ita; kada rana tă yi haske a wannan rana.

  3. Don me aka ba mutum rai, mutumin da bai san wani abu game da kansa ba, mutumin da Allah ya kange shi.

  4. A sa’a ɗaya Allah yake hallaka su, cikin fushinsa yakan hallaka su.

  5. ‘Ko zai yiwu mutum yă fi Allah adalci, ko kuma mutum yă fi wanda ya halicce shi tsarki?

  6. In Allah bai yarda da bayinsa ba, in ya sami mala’ikunsa da laifi,

  7. “Amma da a ce ni ne, da zan roƙi Allah; zan gaya masa damuwata.

  8. Yana ceton matalauta daga takobin da za tă kashe su da shi; yana cetonsu daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi.

  9. “Mai albarka ne wanda Allah yake yi masa gyara in mutumin ya yi kuskure; saboda haka kada ka guje wa horon Maɗaukaki.

  10. Ko da yake yana sa ciwo, shi ne kuma yake warkar da ciwon; ciwon da ya ji maka, shi da kansa zai warkar da shi.

  11. Lokacin yunwa yana tsare ka daga mutuwa, a cikin yaƙi kuma yana kāre ka daga sarar takobi.

  12. Kibiyoyin Maɗaukaki suna a kaina, ruhuna yana shan dafinsa; fushin Allah ya sauka a kaina.

  13. “Kash, da ma Allah zai ba ni abin da nake fatar samu, da ma Allah zai biya mini bukatata,

  14. wato, Allah yă kashe ni, yă miƙa hannunsa yă yanke raina!

  15. Da sai in ji daɗi duk zafin da nake sha ban hana maganar Mai Tsarkin nan cika ba.

  16. “Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki ya rabu ta tsoron Maɗaukaki.

  17. Ni teku ne, ko kuwa dodon ruwa, don me kake tsaro na?

  18. duk da haka kana ba ni tsoro da mafarke-mafarke, kana tsorata ni da wahayi.

  19. “Mene ne mutum har da ka kula da shi haka, har ka mai da hankali a kansa,

  20. har kake duba shi kowace safiya, kake kuma gwada shi koyaushe?

  21. Ba za ka ɗan daina kallo na ba ko ka rabu da ni na ɗan lokaci?

  22. In na yi zunubi, me na yi maka, kai mai lura da mutane? Don me ka sa ni a gaba? Na zame maka kaya mai nauyi ne?

  23. Me ya sa ba za ka gafarta mini laifofina ba? Gama na kusa kwantawa cikin ƙasa; za ka neme ni, amma ba za ka same ni ba.”

  24. Allah ba mai shari’ar gaskiya ba ne? Ko Maɗaukaki yakan yi abin da ba daidai ba?

  25. Lokacin da ’ya’yansa suka yi masa zunubi, yakan bar su su sha wahalar da zunubi yake kawowa.