God
Ayoyin da suka ambaci God
Abin da ya rushe ba a iya ginawa ba; in ya kulle mutum ba a iya buɗe shi a sake shi ba.
Idan ya hana ruwan sama, za a yi fări; in kuma ya saki ruwa za a yi ambaliya.
Shi ne mai ƙarfi da kuma mai nasara; mai ruɗi da wanda aka ruɗa, duk nasa ne.
yana sa al’ummai su zama manya, sai kuma yă hallaka su; yana sa al’ummai su ƙasaita, yă kuma watsar da su.
Suna lallube cikin duhu ba haske; yă sa su yi ta tangaɗi kamar bugaggu.
Amma ina so in yi magana da Maɗaukaki, in kai kukana wurin Allah kai tsaye.
Za ku iya yin muguwar magana a madadin Allah? Ko za ku yi ƙarya a madadinsa?
Ko za ku nuna masa sonkai? Ko za ku yi gardama a madadinsa?
In ya bincike ku zai tarar ba ku da laifi? Ko za ku iya ruɗe shi yadda za ku ruɗi mutane?
Ko ikonsa ba ya ba ku tsoro? Tsoronsa ba zai auka muku ba?
Ko da zai kashe ni ne, begena a cikinsa zai kasance; ba shakka zan kāre kaina a gabansa
lalle wannan zai kawo mini kuɓuta gama ba wani marar tsoron Allah da zai iya zuwa wurinsa!
“Kai dai biya mini waɗannan bukatu biyu kawai ya Allah, ba zan kuwa ɓoye daga gare ka ba;
Ka janye hannunka nesa da ni, ka daina ba ni tsoro da bantsoronka.
Sa’an nan ka kira ni, zan kuwa amsa, ko kuma ka bar ni in yi magana sai ka amsa mini.
Don me ka ɓoye mini fuskarka; ka kuma sa na zama kamar maƙiyinka?
Ko za a wahalar da ganye wanda iska take hurawa? Ko za ka bi busasshiyar ciyawa?
Gama ka rubuta abubuwa marasa daɗi game da ni; ka sa na yi gādon zunuban ƙuruciyata.
Ka daure ƙafafuna da sarƙa; kana kallon duk inda na taka ta wurin sa shaida a tafin ƙafafuna.
Za ka zura ido a kan irin wannan ne? Za ka kawo shi gaba don ka yi masa shari’a?
An lissafta kwanakin mutum; ka riga ka ɗibar masa watanni, ka yi masa iyaka, ba zai iya wuce iyakar ba.
“Da ma za ka ɓoye ni a cikin kabari ka ɓoye ni har sai fushinka ya wuce! In da za ka keɓe mini lokaci sa’an nan ka tuna da ni!
Za ka kira zan kuwa amsa maka; za ka yi marmarin abin da hannunka ya halitta.
Ba shakka a lokacin ne za ka lura da matakaina amma ba za ka kula da zunubaina ba.
Za a daure laifofina a cikin jaka; za ka rufe zunubaina.