Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Zai haras da dukiyar da ya haɗiye; Allah zai sa cikinsa yă haras da su.

  2. Lokacin da ya cika cikinsa, Allah zai zuba fushinsa a kansa, zai daddaka shi.

  3. Ambaliyar ruwa za tă tafi da gidansa, ruwaye masu gudu a ranar fushin Allah.

  4. Abin da Allah zai sa yă faru da mugu ke nan, gādon da Allah ya ba shi ke nan.”

  5. Gidajensu suna zama cikin lafiya ba ruwansu da fargaba. Kuma Allah ba ya ba su horo.

  6. Duk da haka suna ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu.’ Ba ma so mu san hanyoyinka.

  7. Wane ne Maɗaukaki har da za mu bauta masa? Wace riba za mu samu ta wurin yin addu’a gare shi?

  8. “Duk da haka, sau nawa fitilar mugu take mutuwa? Sau nawa bala’i yake auka masa, ko Allah ya taɓa hukunta mugu cikin fushi?

  9. An ce ‘Allah yana tara wa ’ya’yan mutum horon da zai ba mutumin.’ Bari yă ba mutumin horo don yă san ya yi haka!

  10. Bari idanunsa su ga yadda zai hallaka; bari yă sha daga fushin Maɗaukaki.

  11. “Wani zai iya koya wa Allah ilimi tun da yana shari’anta har da waɗanda suke manya masu iko?

  12. “Mutum yana iya zama da amfani a wurin Allah? Mai hikima ma zai iya zama da amfani a wurin shi?

  13. Wane daɗi Allah zai ji in kai mai adalci ne? Wace riba zai samu in rayuwarka marar laifi ce?

  14. “Ko don kana tsoron Allah shi ya sa ya kwaɓe ka ya kuma bari haka yă same ka?

  15. “Ba Allah ne a can sama ba? Dubi yadda taurarin sama suke can nesa a sama!

  16. Duk da haka ka ce, ‘Me Allah ya sani? A cikin duhu ne yake shari’a?

  17. Gajimare ya rufe shi, saboda haka ba ya ganinmu lokacin da yake takawa a cikin sammai.’

  18. Suka ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu! Me Maɗaukaki zai yi mana?’

  19. Duk da haka kuwa shi ne ya cika gidajensu da abubuwa masu kyau, saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye.

  20. “Ka miƙa kanka ga Allah ka samu salamarsa; ta haka ne arziki zai zo maka.

  21. Ka bi umarnin da zai fito daga bakinsa kuma ka riƙe maganarsa a cikin zuciyarka.

  22. In ka komo ga Maɗaukaki, za ka warke. In ka kawar da mugunta daga cikin gidanka.

  23. sa’an nan ne Maɗaukaki zai zama zinariyarka, zai zama azurfa mafi kyau a wurinka.

  24. Ba shakka a lokacin ne za ka sami farin ciki daga wurin Maɗaukaki, ku kuma ɗaga idanunku ga Allah

  25. Za ka yi addu’a zuwa gare shi, zai kuwa ji ka, kuma za ka cika alkawuranka.