Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ya rufe fuskar wata, ya shimfiɗa gizagizai a kan shi,

  2. Madogaran sama sun girgiza, saboda tsawatawarsa.

  3. Da ikonsa ya kwantar da teku; da hikimarsa ya hallaka dodon ruwan nan Rahab.

  4. Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi kyau da hannunsa ya soke macijin nan mai gudu.

  5. Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin ayyukansa masu yawa. Kaɗan kawai muke ji game da shi! Wane ne kuwa yake iya gane tsawar ikonsa?”

  6. “Na rantse da Allah mai rai, wanda ya danne mini gaskiyata, Maɗaukaki, wanda ya sa nake cikin ɗacin rai.

  7. Muddin ina da rai a cikina kuma numfashin Allah yana cikin hancina,

  8. Ba zan taɓa yarda cewa kuna da gaskiya ba; har in mutu, ba zan daina kāre mutuncina ba.

  9. Gama wane bege marar tsoron Allah yake da shi, lokacin da aka datse shi, lokacin da Allah ya ɗauke ransa?

  10. Ko Allah yana sauraron kukansa lokacin da ƙunci ya auko masa?

  11. Ko zai sami farin ciki daga Maɗaukaki? Ko zai yi kira ga Allah a kowane lokaci?

  12. “Zan koya muku game da ikon Allah; ba zan ɓoye hanyoyin Maɗaukaki ba.

  13. “Ga abin da mugaye za su samu gādon da azzalumi zai samu daga Maɗaukaki.

  14. Za tă murɗe shi ba tausayi, lokacin da yake guje wa ikon iskar.

  15. Hannun mutum ya iya sarrafa ƙanƙarar duwatsu, yă kuma tumɓuke tushen duwatsu.

  16. Yana tona rami a cikin duwatsu idanunsa suna ganin dukan dukiyar da ke cikin duwatsun.

  17. Yana nema daga ina ruwan rafi yake ɓulɓulowa yana kuma binciko abubuwan da suke a ɓoye yă kawo su cikin haske.

  18. Allah ya gane hanyar zuwa wurinta. Shi ne kaɗai ya san inda take zama,

  19. Gama yana ganin iyakar duniya kuma yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sama.

  20. Lokacin da ya yi iska ya sa ta hura, ya kuma auna ruwaye.

  21. Lokacin da ya yi wa ruwan sama doka da kuma hanya domin walƙiya,

  22. sai ya dubi hikima ya auna ta; ya tabbatar da ita, ya gwada ta.

  23. Ya kuma ce wa mutum, ‘Tsoron Ubangiji shi ne hikima, kuma guje wa mugunta shi ne fahimi.’ ”

  24. “Da ma ina nan lokacin da ya wuce baya can, kwanakin da Allah yake lura da ni,

  25. lokacin da fitilarsa take haske a kaina na yi tafiya cikin duhu tare da haskensa.