Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Gama Allah yana magana, yanzu ga wannan hanya, yanzu kuma ga wata hanya ko da yake ba lalle mutum yă lura ba.

  2. mai yiwuwa yă yi musu magana a cikin kunnuwansu yă razana su da gargaɗinsa,

  3. don a juyar da su daga abin da yake yi da ba daidai ba a kuma hana su daga girman kai,

  4. yă yi masa alheri yă ce, ‘Kada ka bari yă fāɗa cikin rami, na samu fansa dominsa.’

  5. Ya yi addu’a ga Allah ya kuwa samu alheri a wurinsa, yana ganin fuskar Allah yana kuma yin sowa don murna; Allah ya mayar da shi ya zama mai adalci.

  6. “Allah ya yi wa mutum duk waɗannan, sau biyu, har ma sau uku.

  7. “Ayuba ya ce, ‘Ba ni da laifi, amma Allah ya hana mini hakkina.

  8. Gama ya ce, ‘Ba ribar da mutum zai samu lokacin da yake ƙoƙari yă faranta wa Allah zuciya.’

  9. “Saboda haka ku saurare ni, ku masu ganewa. Ko kaɗan Allah ba ya mugunta, Maɗaukaki ba ya kuskure.

  10. Yana biyan mutum bisa ga abin da ya yi; yana kawo masa abin da ayyukansa suka jawo.

  11. Ba zai yiwu Allah yă yi ba daidai ba, Maɗaukaki ba zai yi shari’a marar gaskiya ba.

  12. Wane ne ya ba shi iko yă lura da duniya? Wane ne ya ba shi iko kan dukan duniya?

  13. In nufinsa ne ya kuma janye ruhunsa da numfashinsa,

  14. Maƙiyin gaskiya zai iya yin mulki? Za ka iya ba mai gaskiya, Maɗaukaki laifi?

  15. wanda ba ya nuna sonkai ga ’ya’yan sarki kuma ba ya goyon bayan masu arziki a kan matalauta, gama dukansu shi ya yi su da hannuwansa.

  16. “Idanunsa suna kan al’amuran mutane; yana ganin tafiyarsu duka.

  17. Allah ba ya bukata yă ci gaba da bincike mutane, har da za su zo gabansa don yă shari’anta su.

  18. Gama yana sane da abubuwan da suke yi, yana hamɓarar da su da dare a kuma ragargaza su.

  19. domin sun juya daga binsa, kuma ba su kula da hanyoyinsa ba.

  20. Sun sa kukan matalauta ya kai wurinsa yadda ya kai ga jin kukan masu bukata.

  21. Amma in ya yi shiru, wa zai ba shi laifi? In ya ɓoye fuskarsa, wa zai gan shi? Duk da haka shi yake da iko kan mutum da al’umma duka,

  22. “A ce mutum ya ce wa Allah, ‘Na yi laifi, amma ba zan sāke saɓa wa wani ba.

  23. Ka koya mini abin da ba zan iya gani ba; in na yi ba daidai ba, ba zan sāke yi ba.’

  24. Ya kamata Allah yă yi maka bisa ga abin da ka ce ne, sa’ad da ka ƙi ka tuba? Dole kai ka zaɓa, ba ni ba; yanzu ka gaya mini abin da ka sani.

  25. Ya ƙara tawaye a kan zunubansa; ya tafa hannuwansa na reni a cikinmu ya kuma ƙara yawan maganganunsa ga Allah.”