God
Ayoyin da suka ambaci God
“Ko kana tsammani wannan gaskiya ne? Kana cewa, ‘Ni mai adalci ne a gaban Allah.’
In kun yi zunubi ta yaya wannan zai shafi Allah? In zunubanku sun yi yawa, me wannan zai yi masa?
In kuna da adalci, me kuka ba shi, ko kuma me ya karɓa daga hannunku?
Amma ba wanda ya ce, ‘Ina Allah wanda ya halicce ni, mai ba da waƙoƙi cikin dare,
Lalle Allah ba ya sauraron roƙonsu na wofi; Maɗaukaki ba ya kula da roƙonsu.
Ta yaya zai saurara sosai ko zai saurara lokacin da kake cewa ba ka ganinsa, cewa ka kawo ƙara a wurinsa kuma dole ka jira shi.
Kuma ka ce, ba ya ba da horo cikin fushinsa ko kaɗan ba ya kula da mugunta.
“Ka ɗan ƙara haƙuri da ni kaɗan, zan kuma nuna maka cewa akwai sauran abubuwan da zan faɗa a madadin Allah.
Abin da zan gaya maka ba ƙarya ba ne; mai cikakken sani yana tare da kai.
“Allah mai iko ne, amma ba ya rena mutane; shi mai girma ne cikin manufarsa.
Ba ya fasa duban masu adalci; yana sa su tare da sarakuna yana ɗaukaka su har abada.
yana gaya musu abin da suka yi, cewa sun yi zunubi da girman kai.
In sun yi biyayya suka bauta masa, za su yi rayuwa dukan kwanakinsu cikin wadata shekarunsu kuma cikin kwanciyar zuciya.
“Waɗanda ba su da Allah a zuciyarsu su ne suke riƙe fushi; ko sa’ad da ya ba su horo, ba su neman taimakonsa.
“Yana so yă rinjaye ka daga haƙoran ƙunci, zuwa wuri mai sauƙi inda ba matsi zuwa teburinka cike da abincin da kake so.
Ka yi hankali kada wani yă ruɗe ka da arziki; kada ka bar toshiya ta sa ka juya.
Dukiyarka ko dukan yawan ƙoƙarinka sun isa su riƙe ka su hana ka shan ƙunci?
“An ɗaukaka Allah cikin ikonsa. Wane ne malami kamar sa?
Wane ne ya nuna masa hanyar da zai bi, ko kuma wane ne ya ce masa, ‘Ba ka yi daidai ba?’
Ka tuna ka ɗaukaka aikinsa, waɗanda mutane suka yaba a cikin waƙa.
Allah mai girma ne, ya wuce ganewarmu! Yawan shekarunsa ba su bincikuwa.
“Yana sa ruwa yă zama tururi yă zubo daga sama.
Wane ne zai iya gane yadda ya shimfiɗa gizagizai yadda yake tsawa daga wurin zamansa?
Dubi yadda ya baza walƙiyarsa kewaye da shi, tana haskaka zurfin teku.
Haka yake mulkin al’ummai yana kuma tanada abinci a wadace.