Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Musa ya ce wa Allah, “A ce ma na tafi wurin Isra’ilawa na ce musu, ‘Allah na kakanninku ya aiko ni wurinku,’ in suka tambaye ni, ‘Mene ne sunansa?’ Me zan ce?”

  2. Allah ya ce wa Musa, “NI NE wanda NINE. Abin da za ka faɗa wa Isra’ilawa ke nan cewa, ‘NI NE, ya aiko ni wurinku.’ ”

  3. Allah ya kuma ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ubangiji, Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub, ya aiko ni wurinku.’ Wannan shi ne sunana har abada, sunan da za a tuna da ni daga tsara zuwa tsara ke nan.

  4. “Tafi ka tattara dattawan Isra’ila, ka ce musu, ‘Ubangiji, Allah na kakanninku, Allah na Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, ya bayyana a gare ni ya ce, Na lura da ku, na kuma ga abubuwan da ake yi muku a Masar.

  5. Na kuma yi alkawari, zan fitar da ku daga azabarku a Masar zuwa ƙasar Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa, ƙasa mai zub da madara da zuma.’

  6. “Dattawan Isra’ila za su saurare ka. Sa’an nan da kai da dattawan Isra’ila, za ku tafi wurin sarkin Masar, ku ce masa, ‘Ubangiji, Allah na Ibraniyawa, ya sadu da mu. Bari mu yi tafiyar kwana uku zuwa cikin hamada domin mu yi hadaya wa Ubangiji Allahnmu.’

  7. Amma na san cewa sarkin Masar ba zai yarda ku tafi ba, sai hannu mai ƙarfi ya tilasta shi.

  8. Saboda haka zan miƙa hannuna in bugi Masarawa da duk al’ajaban da zan aikata a cikinsu. Bayan haka zai bar ku, ku tafi.

  9. “Zan kuma sa mutanen su sami tagomashi daga wurin Masarawa, saboda sa’ad da za ku fita, ba za ku fita hannu wofi ba.

  10. Musa ya amsa ya ce, “In ba su gaskata ni ba, suka kuma ce, ‘Ubangiji bai bayyana gare ka ba fa’?”

  11. Sai Ubangiji ya ce, “Mene ne wannan a hannunka?” Musa ya amsa ya ce, “Sanda.”

  12. Sai Ubangiji ya ce, “Jefa shi ƙasa.” Musa ya jefa shi ƙasa, sai sandan ya zama maciji, Musa kuwa ya gudu daga gare shi.

  13. Sai Ubangiji ya ce masa, “Sa hannunka ka ɗauke shi ta wutsiya.” Sai Musa ya miƙa hannu, ya kama macijin, macijin kuwa ya dawo sanda a hannunsa.

  14. Ubangiji ya ce, “Wannan zai sa su ba da gaskiya cewa Ubangiji, Allah na kakanninsu, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da kuma Allah da Yaƙub, ya bayyana gare ka.”

  15. Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Sa hannunka cikin rigarka.” Sai Musa ya sa hannunsa cikin rigarsa, sa’ad da ya fitar da shi, sai hannun ya a kuturce fari fat, kamar ƙanƙara.

  16. Sai Ubangiji ya ce, “Yanzu, mayar da hannunka a rigarka.” Sai Musa ya sa hannunsa cikin rigarsa, da ya fitar da shi, sai hannun ya koma kamar sauran jikinsa.

  17. Musa ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji, ni ban mai iya magana ba ne, ban taɓa iya ba, ko a yanzu ma, bayan ka yi magana da ni, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma.”

  18. Ubangiji ya ce masa, “Wa ya ba mutum bakinsa? Wa yake maishe shi kurma ko bebe? Wa yake ba shi gani ko yă makanta shi? Ashe ba Ni Ubangiji ba ne?

  19. Yanzu tafi, zan taimake ka ka yi magana, zan kuma koya maka abin da za ka faɗa.”

  20. Amma Musa ya ce, “Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka nemi wani ka aika.”

  21. Sai Ubangiji ya yi fushi da Musa ya ce, “Ɗan’uwanka Haruna Balawe, ba ya nan ne? Na san ya iya magana. Ya riga ya kama hanya don yă sadu da kai, zai kuma yi farin ciki sa’ad da ya gan ka.

  22. Za ka yi masa magana. Ka kuma sa masa maganata a baki; zan kuma taimake ku magana, in koya muku abin da za ku yi.

  23. Zai yi magana da mutane a madadinka, zai zama kamar bakinka, kai kuwa kamar Allah a gare shi.

  24. Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa a Midiyan, “Koma Masar, domin dukan mutanen da suke neman su kashe ka sun mutu.”

  25. Sai Musa ya ɗauki matarsa da ’ya’yansa maza, ya sa su a kan jaki, suka kama hanya zuwa Masar. Ya kuma ɗauki sandan Allah a hannunsa.