Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Dalilin da aka ba wa Fir’auna mafarkan nan kashi biyu kuwa shi ne cewa Allah ya riga ya ƙaddara al’amarin. Allah zai aikata shi, ba da daɗewa ba.

  2. Saboda haka Fir’auna ya tambaye su, “Za mu iya samun wani kamar wannan mutum, wannan wanda Ruhun Allah yake cikinsa?”

  3. Sai Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Da yake Allah ya ba ka sanin dukan waɗannan, babu wani mai basira da kuma hikima kamar ka.

  4. Yusuf ya ba wa ɗansa na fari suna Manasse ya ce, “Gama Allah ya sa na mance dukan wahalata da dukan gidan mahaifina.”

  5. Ya ba wa ɗansa na biyu suna Efraim ya ce, “Gama Allah ya wadata ni cikin wahalata.”

  6. A rana ta uku, Yusuf ya ce musu, “Ku yi wannan za ku kuwa rayu, gama ina tsoron Allah.

  7. Sai ya ce wa ’yan’uwansa, “An mayar mini da azurfata. Ga shi a cikin buhuna.” Zuciyarsu ta karai, suka dubi juna suna rawan jiki, suka ce, “Mene ne wannan da Allah ya yi mana?”

  8. Bari Allah Maɗaukaki yă nuna muku alheri a gaban mutumin saboda yă bar ɗan’uwanku da Benyamin su dawo tare da ku. Ni kuwa, in na yi rashi, na yi rashi.”

  9. Sai mai hidimar ya ce, “Ba kome, kada ku ji tsoro. Allahnku, Allahn mahaifinku ne ya ba ku dukiyar a cikin buhunanku; ni dai, na karɓi azurfanku.” Sa’an nan ya fitar musu da Simeyon.

  10. Da ya ɗaga idanu, sai ya ga ɗan’uwansa Benyamin, ɗan mahaifiyarsa, sai ya yi tambaya, “Wannan ne ƙaramin ɗan’uwanku, wanda kuka faɗa mini a kai?” Ya kuma ce, “Allah yă yi maka albarka, ɗana.”

  11. Amma suka ce masa, “Me ya sa ranka yă daɗe yake faɗin irin waɗannan abubuwa? Allah yă sawwaƙe bayinka su yi irin wannan abu!

  12. Yahuda ya amsa ya ce, “Me za mu ce wa ranka yă daɗe? Yaya kuma za mu wanke kanmu daga wannan zargi? Allah ya tona laifin bayinka. Ga mu, za mu zama bayinka, da mu da wanda aka sami kwaf ɗin a hannunsa.”

  13. Amma Yusuf ya ce, “Allah yă sawwaƙe in yi haka! Mutumin da aka sami kwaf ɗin a hannunsa ne kaɗai zai zama bawana. Sauranku, ku koma ga mahaifinku da salama.”

  14. Yanzu dai, kada ku damu, kada kuma ku yi fushi da kanku saboda kun sayar da ni a nan, gama Allah ya aiko ni gabanku ne don in ceci rayuka.

  15. Amma Allah ya aiko ni gabanku ne don in adana muku raguwa a duniya, in kuma ceci rayukanku ta wurin ceto mai girma.

  16. “Saboda haka fa, ba ku ba ne kuka aiko ni nan, Allah ne. Ya mai da ni mahaifi ga Fir’auna, shugaban dukan gidansa da kuma mai mulkin dukan Masar.

  17. Yanzu sai ku gaggauta zuwa wurin mahaifina ku faɗa masa, ‘Abin da ɗanka Yusuf ya ce; Allah ya mai da ni shugaban dukan Masar. Gangaro wurina; kada ka jinkirta.

  18. Saboda haka Isra’ila ya kama hanya da dukan abin da yake nasa, sa’ad da ya kai Beyersheba, sai ya miƙa hadayu ga Allah na Ishaku, mahaifinsa.

  19. Allah kuwa ya yi magana ga Isra’ila a wahayi da dare ya ce, “Yaƙub! Yaƙub!” Yaƙub kuwa ya amsa ya ce, “Ga ni.”

  20. Sai Allah ya ce, “Ni ne Allah, Allah na mahaifinka. Kada ka ji tsoron zuwa Masar, gama zan mai da kai al’umma mai girma a can.

  21. Yaƙub ya ce wa Yusuf, “Allah Maɗaukaki ya bayyana gare ni a Luz a ƙasar Kan’ana, a can ya albarkace ni

  22. Yusuf ya ce wa mahaifinsa, “Su ne ’ya’yan da Allah ya ba ni a nan.” Sa’an nan Isra’ila ya ce, “Kawo mini su saboda in albarkace su.”

  23. Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Ban yi tsammani zan ga fuskarka kuma ba, yanzu kuwa Allah ya bar ni in ga ’ya’yanka su ma.”

  24. Sa’an nan ya albarkaci Yusuf ya ce, “Bari Allah a gaban wanda kakannina Ibrahim da Ishaku suka yi tafiya, Allahn da ya zama makiyayina dukan raina zuwa wannan rana,

  25. Ya albarkace su a wannan rana ya ce, “A cikin sunanku Isra’ila zai sa wannan albarka ‘Bari Allah yă sa ku zama kamar Efraim da Manasse.’ ” Saboda haka ya sa Efraim gaban Manasse.