Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Sai Dawuda ya yi wa matarsa Batsheba ta’aziyya, ya kuma tafi wurinta ya kwana da ita. Ta kuma haifi ɗa, suka ba shi suna Solomon. Ubangiji ya ƙaunace shi;

  2. kuma saboda Ubangiji ya ƙaunace shi, sai ya aika da saƙo ta wurin annabi Natan yă ba shi suna Yedidiya.

  3. Sai ta ce, “To, bari sarki yă rantse da Ubangiji Allahnsa don yă hana mai ramako yin ƙarin hallakawar da aka yi, domin kada a hallaka ɗana.” Sai ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, babu gashi guda na ɗanki da zai fāɗi ƙasa.”

  4. Matar ta ce, “To, don me ka yi wa mutanen Allah irin wannan abu? Sa’ad da sarki ya ce haka, ashe, ba ka hukunta kanka ke nan ba, tun da yake sarki bai yarda ɗansa yă komo gida ba?

  5. Kamar ruwan da ya zuba a ƙasa, wanda ba a iya kwasa, haka dole mu mutu. Amma Allah ba ya ɗaukan rai; a maimako, yakan ƙirƙiro hanyoyi domin mutumin da aka kora kada yă kasance yasasshe daga gare shi.

  6. Wataƙila sarki zai yarda yă ceci baiwarsa daga hannun mutumin nan da yake ƙoƙari yă hallaka ni da ɗana daga gādon da Allah ya ba mu.’

  7. “Yanzu kuwa baiwarka tana cewa, ‘Bari magana ranka yă daɗe sarki yă ba ni hutu, gama ranka yă daɗe sarki yana kama da mala’ikan Allah cikin rarrabe nagarta da mugunta. Bari Ubangiji Allahnka yă kasance tare da kai.’ ”

  8. Bawanka Yowab ne ya yi haka don yă daidaita al’amura. Ranka yă daɗe yana da hikima iri ta mala’ikan Allah, ya san dukan kome da yake faruwa a ƙasar.”

  9. A ƙarshen shekara huɗu, Absalom ya ce wa sarki, “Bari in tafi Hebron in cika alkawarin da na yi wa Ubangiji.

  10. Yayinda bawanka yake zama a Geshur, a Aram, na yi wannan alkawari, na ce, ‘In Ubangiji ya komo da ni Urushalima, zan yi wa Ubangiji sujada a Hebron.’ ”

  11. Amma Ittai ya ce wa sarki, “Muddin Ubangiji yana a raye kuma muddin ranka yă daɗe yana a raye, duk inda ranka yă daɗe sarki zai kasance, ko a yi rai ko a mutu, a can bawanka zai kasance.”

  12. Zadok yana nan tare da su, kuma dukan Lawiyawan da suke tare da shi kuwa suna ɗauke da akwatin alkawarin Allah. Suka sauke akwatin alkawarin Allah, Abiyatar ya miƙa hadaya sai da mutane suka gama fita daga birnin.

  13. Sa’an nan sarki ya ce wa Zadok, “Ka komar da akwatin alkawarin Allah cikin birnin. Idan na sami tagomashi a idon Ubangiji, zai dawo da ni, yă kuma sa in sāke gan shi a mazauninsa.

  14. Amma in ya ce, ‘Ina baƙin ciki da kai,’ to, ina a shirye; bari yă yi abin da ya fi masa.”

  15. Saboda haka Zadok da Abiyatar suka ɗauki akwatin alkawarin Allah suka komar da shi Urushalima, suka zauna a can.

  16. To, an gaya wa Dawuda cewa, “Ahitofel yana cikin waɗanda suka hadasa maƙarƙashiya tare da Absalom.” Saboda haka Dawuda ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji ka mai da shawarar Ahitofel ta zama shiririta.”

  17. Da Dawuda ya isa ƙwanƙoli, inda mutane sun saba yi wa Allah sujada, Hushai, mutumin Arkitawa kuwa yana can don yă tarye shi, taguwarsa a yage, ga kuma ƙura a kansa.

  18. Ubangiji ya kama ka saboda alhakin jinin gidan Shawulu, wanda kake sarauta a maimakonsa. Ubangiji ya ba da masarautar ga ɗanka Absalom. Hallaka ta zo maka domin kai mai kisankai ne!”

  19. Amma sarki ya ce, “Ba ruwana da ku, ku ’ya’yan Zeruhiya. Idan yana la’ana ne domin Ubangiji ya ce masa, ‘La’anci Dawuda,’ wa zai ce, ‘Don me kake haka?’ ”

  20. Sa’an nan Dawuda ya ce wa Abishai da dukan fadawansa, “Ɗana, na cikina, yana ƙoƙari yă kashe ni. Balle wannan mutumin Benyamin! Ku ƙyale shi, yă yi ta zargi, Ubangiji ne ya ce masa yă yi haka.

  21. Mai yiwuwa Ubangiji yă ga azabata, yă sāka mini da alheri saboda la’anar da nake sha a yau.”

  22. Sai Hushai mutumin Arkitawa, abokin Dawuda ya je wurin Absalom ya ce masa, “Ran sarki yă daɗe! Ran sarki yă daɗe!”

  23. Hushai ya ce wa Absalom, “A’a, ai, wanda Ubangiji ya zaɓa ta wurin waɗannan mutane, da kuma ta wurin dukan mutane Isra’ila, shi zan zama nasa, zan kuma kasance tare da shi.

  24. To, a kwanakin nan shawarar da Ahitofel yakan bayar takan zama kamar wadda aka nemi daga Allah ne. Haka Dawuda da Absalom duk suke ɗaukan dukan shawarar Ahitofel.

  25. Absalom da dukan mutanen Isra’ila suka ce, “Shawarar Hushai mutumin Arkitawa ta fi ta Ahitofel kyau.” Gama Ubangiji ya ƙudura yă wofinta kyakkyawar shawarar Ahitofel, don yă jawo wa Absalom masifa.