Tsallake zuwa abun ciki

God

11,427 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci God

Tace bisa littafi
  1. Ahimawaz ɗan Zadok ya ce, “Bari in ruga in kai wa sarki labari cewa Ubangiji ya cece shi daga hannun abokan gābansa.”

  2. Sai Ahimawaz ya tā da murya ya ce wa sarki, “Kome lafiya yake!” Sai ya rusuna har ƙasa a gaban sarki ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka! Ya ba da mutanen da suka tayar wa ranka yă daɗe a hannunsa.”

  3. Sai ga mutumin Kush ya iso ya ce, “Ranka yă daɗe sarki, ka ji labari mai kyau! Ubangiji ya cece ka yau daga dukan waɗanda suka tayar maka.”

  4. Sai gaban sarki ya faɗi. Ya haura zuwa ɗakin da yake kan katangar hanyar shiga ya yi kuka. Yayinda yake tafiya ya ce, “Ya ɗana Absalom! Ɗana, ɗana Absalom! Da ma a ce ni ne na mutu maimakonka. Ya Absalom, ɗana, ɗana!”

  5. Yanzu ka fita ka ƙarfafa mutanenka. Na rantse da Ubangiji, in ba ka fita ba, babu mutum guda da za a bari tare da kai a daren nan. Wannan zai fi maka muni fiye da kowace irin masifar da ta auko maka tun ƙuruciyarka har zuwa yanzu.”

  6. Ku kuma ce wa Amasa, ‘Ashe, kai ba jikina ba ne da jinina? Allah yă hukunta ni, da hukunci mai tsanani, idan daga yanzu ba ka zama komandan sojojina a maimakon Yowab ba.’ ”

  7. Sai Abishai ɗan Zeruhiya ya ce, “Bai kamata a kashe Shimeyi saboda wannan ba? Ya la’anci shafaffe na Ubangiji.”

  8. Ya kuwa ɓata suna bawanka a gaban ranka yă daɗe, sarki. Ranka yă daɗe, sarki yana kama da mala’ikan Allah, ka yi abin da ka ga ya fi maka kyau.

  9. Mu ne masu salama da kuma amintattu na Isra’ila. Kana ƙoƙari ka hallaka birnin da yake uwa a Isra’ila. Don me kake so ka hallakar da gādon Ubangiji?”

  10. Lokacin da Dawuda yake mulki, an yi yunwa shekara uku a jere; saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji. Ubangiji ya ce, “Saboda Shawulu ne da alhakin jinin gidansa; domin ya kashe Gibeyonawa.”

  11. Dawuda ya ce wa Gibeyonawa, “Me zan yi muku? Yaya zan yi kafara domin ku sa wa masu gādon Ubangiji albarka?”

  12. a ba mu zuriyarsa maza bakwai, mu kashe su, mu kuma rataye jikunansu a gaban Ubangiji a Gibeya na Shawulu wannan zaɓaɓɓen Ubangiji.” Sai sarki ya ce, “Zan ba ku su.”

  13. Sarki ya ware Mefiboshet ɗan Yonatan jikan Shawulu, saboda rantsuwar da take tsakanin Dawuda da Yonatan, ɗan Shawulu a gaban Ubangiji.

  14. Ya ba da su ga Gibeyonawa, waɗanda suka kashe su, suka kuma rataye jikunansu a gaban Ubangiji. Dukan bakwai ɗin an kashe su gaba ɗaya; an kashe su a farkon kwanankin girbi, daidai lokacin fara girbin sha’ir.

  15. Suka binne ƙasusuwan Shawulu da na ɗansa Yonatan a kabarin Kish, mahaifin Shawulu, a Zela a Benyamin. Suka kuma yi kome da sarki ya umarta. Bayan wannan Allah ya ji addu’arsu a madadin ƙasar.

  16. Dawuda ya rera wannan waƙa ga Ubangiji, sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa, da kuma daga hannun Shawulu.

  17. Ya ce, “Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona;

  18. Allahna shi ne dutsena. A gare shi nake samun kāriya shi ne garkuwata da kuma ƙahon cetona. Shi ne mafakata, maɓuyata, da mai cetona. Daga mutane masu fitina, ka cece ni.

  19. “Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo, na kuwa tsira daga abokan gābana.

  20. “A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; na yi kira ga Allahna. Daga cikin haikalinsa ya saurare muryata; kukata ta zo kunnensa.

  21. Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza, harsashan sararin sama sun jijjigu; suka yi makyarkyata saboda yana fushi.

  22. Hayaƙi ya taso daga kafaffen hancinsa; harshen wuta mai cinyewa daga bakinsa, garwashi mai ƙuna daga bakinsa.

  23. Ya buɗe sararin sama, ya sauko ƙasa, girgije mai duhu suna ƙarƙashin ƙafafunsa.

  24. Ya hau kerubobi, ya tashi sama; ya yi firiya a fikafikan iska.

  25. Ya mai da duhu abin rufuwarsa gizagizai masu kauri cike da ruwa suka kewaye shi.