God
Ayoyin da suka ambaci God
Daga cikin hasken gabansa garwashi wuta mai ci ya yi walƙiya.
Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama; aka ji muryar Mafi Ɗaukaka.
Ya harbe kibiyoyi, ya wartsar da abokan gāba, da walƙiya kuma ya sa suka gudu.
Aka bayyana kwarin teku, tushen duniya suka tonu. A tsawatawar Ubangiji, da numfashinsa mai ƙarfi daga hancinsa.
“Daga sama ya miƙo hannu ya ɗauke ni, ya tsamo ni daga zurfafa ruwaye.
Suka auka mini cikin ranar masifata, amma Ubangiji ya kiyaye ni.
Ya fito da ni, ya kai ni wuri mafi fāɗi; ya kuɓutar da ni gama yana jin daɗina.
“Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina; bisa ga tsabtar hannuwana ya sāka mini.
Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji; ban yi wani mugun abu da zai juyar da ni daga Allahna ba.
Dukan dokokinsa suna a gabana; ban ƙi ko ɗaya daga umarnansa ba.
Ba ni da laifi a gabansa na kiyaye kaina daga yin zunubi.
Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina bisa ga tsarkina a gabansa.
“Ga masu aminci, kakan nuna kanka mai aminci, ga marasa laifi, kakan nuna kanka marar laifi,
ga masu tsarki, kakan nuna musu tsarki. Amma ga masu karkataccen hali, kakan nuna kanka mai wayo.
Kakan ceci mai tawali’u, amma idanunka suna a kan masu girman kai don ka ƙasƙantar da su.
Ya Ubangiji kai ne fitilata; Ubangiji ya mai da duhuna haske.
Da taimakonka zan iya auka wa rundunar sojoji; tare da Allahna zan iya hawan katanga.
“Ga Allah dai, hanyarsa cikakkiya ce; maganar Ubangiji babu kuskure. Shi garkuwa ce ga waɗanda suka nemi mafaka a gare shi.
Gama wane ne Allah, in ba Ubangiji ba? Wane ne dutse kuma in ba Allahnmu ba?
Allah ne ya ba ni ƙarfi, ya kuma mai da hanyata cikakkiya.
Ka ba ni garkuwar nasararka; ka sauko don ka sa in sami girma.
Ka ba ni ƙarfi don yaƙi; ka sa maƙiyina suka rusuna a ƙafafuna.
Suka nemi taimako, amma babu wanda zai cece su, suka yi kira ga Ubangiji, amma ba a amsa musu ba.
“Ubangiji yana a raye! Yabo ta tabbata ga Dutsena! Ɗaukaka ga Allah, Dutse, Mai Cetona!
Shi ne Allahn da yake rama mini, wanda ya sa al’ummai a ƙarƙashina,