Tsallake zuwa abun ciki

Ephraim

160 ayoyi · 9 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Ephraim

Tace bisa littafi
  1. Girmankan Isra’ila yana ba da shaida a kansu; Isra’ilawa, har ma Efraim, sun yi tuntuɓe a cikin zunubinsu; Yahuda ma ya yi tuntuɓe tare da su.

  2. Efraim za tă zama kango a ranar hukunci. A cikin kabilan Isra’ila na yi shelar abin da yake tabbatacce.

  3. An danne Efraim, an murƙushe ta a shari’a ta ƙudura ga bin gumaka.

  4. Na zama kamar asu ga Efraim, kamar ruɓa ga mutanen Yahuda.

  5. “Sa’ad da Efraim ya ga ciwonsa, Yahuda kuwa miyakunta, sai Efraim ya juya ga Assuriya, ya aika wurin babban sarki don neman taimako. Amma bai iya warkar da kai ba, bai iya warkar da miyakunka ba.

  6. Gama zan zama kamar zaki ga Efraim, kamar babban zaki ga Yahuda. Zan yage su kucu-kucu in tafi; zan kwashe su, ba wanda zai kuɓutar da su.

  7. “Me zan yi da kai Efraim? Me zan yi da kai Yahuda? Ƙaunarku tana kamar hazon safiya, kamar raɓar safiya da takan ɓace.

  8. Na ga wani abu mai bantsoro a gidan Isra’ila. A can Efraim ya miƙa wuya ga karuwanci Isra’ila kuma ta ƙazantu.

  9. a duka sa’ad da zan warkar da Isra’ila, zunuban Efraim za su tonu za a kuma bayyana laifofin Samariya. Suna ruɗu, ɓarayi sukan fasa su shiga gidaje, ’yan fashi sukan yi fashi a tituna;

  10. “Efraim yana cuɗanya da al’ummai; Efraim waina ne mai fāɗi da ba a juye ba.

  11. “Efraim yana kama da kurciya, marar wayo, marar hankali, yanzu yana kira ga Masar, yanzu yana juyewa ga Assuriya.

  12. Gama sun haura zuwa Assuriya kamar jakin jejin da yake yawo shi kaɗai. Efraim ya sayar da kansa ga maza.

  13. “Ko da yake Efraim ya gina bagadai masu yawa don hadayun zunubi, waɗannan sun zama bagade don yin zunubi.

  14. Ba za su ci gaba da zama a ƙasar Ubangiji ba; Efraim zai koma Masar yă kuma ci abinci marar tsarki a Assuriya.

  15. Annabi, tare da Allahna, su ne masu tsaro a bisa Efraim, duk da haka tarko na jiransa a dukan hanyoyi, da kuma ƙiyayya a cikin gidan Allahnsa.

  16. Darajar Efraim za tă yi firiya tă tafi kamar tsuntsu, ba haihuwa, ba juna biyu, ba ɗaukar ciki.

  17. Na ga Efraim, kamar birnin Taya, da aka kafa a wuri mai daɗi. Amma Efraim zai fitar da ’ya’yansu ga masu yanka.”

  18. An ka da Efraim, saiwarsu ta bushe, ba sa ba da amfani. Ko da sun haifi ’ya’ya zan kashe waɗanda suka fi ƙauna.”

  19. Za a ɗauke shi a kai Assuriya kamar gandu wa babban sarki. Efraim zai sha kunya; Isra’ila zai sha kunya saboda gumakan itacensa.

  20. Efraim horarriyar karsana ce mai son sussuka; saboda haka zan sa karkiya a kyakkyawan wuyanta. Zan bi da Efraim, Dole Yahuda yă yi noma, dole kuma Yaƙub yă ja garman noma.

  21. Ni ne na koya wa Efraim tafiya ina kama su da hannu; amma ba su gane cewa ni ne na warkar da su ba.

  22. “Yaya zan ba da kai, Efraim? Yaya zan miƙa ka, Isra’ila? Yaya zan yi da kai kamar Adma? Yaya zan yi da kai kamar Zeboyim? Zuciyata ta canja a cikina; dukan tausayina ya huru.

  23. Ba zan zartar da fushina mai zafi ba, ba kuwa zan juya in ragargaza Efraim ba. Gama ni Allah ne, ba mutum ba, Mai Tsarki a cikinku. Ba zan zo cikin fushi ba.

  24. Mutanen Efraim sun kewaye ni da ƙarairayi, gidan Isra’ila da ruɗu. Mutanen Yahuda kuma suna yi wa Allah ƙin ji, har ma a kan Mai Tsarkin nan mai aminci.

  25. Efraim yana kiwo a kan iska; yana fafarar iskar gabas dukan yini yana riɓaɓɓanya ƙarairayi da rikici. Ya yi yarjejjeniya da Assuriya ya kuma aika wa Masar man zaitun.