Tsallake zuwa abun ciki

David

968 ayoyi · 40 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci David

Tace bisa littafi
  1. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi; Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala.

  2. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da annabi Natan ya zo wurinsa bayan Dawuda ya yi zina da Batsheba. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa; bisa ga tausayinka mai girma ka shafe laifofina.

  3. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Wani maskil ta Dawuda. Sa’ad da Doyeg mutumin Edom ya tafi wurin Shawulu ya ce masa, “Dawuda ya tafi gidan Ahimelek.” Me ya sa kake fariya game da mugunta, kai babban mutum? Me ya sa kake fariya dukan yini, kai da kake abin kunya a idanun Allah?

  4. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat. Wani maskil na Dawuda. Wawa ne kawai yakan ce a zuciyarsa, “Ba Allah.” Sun lalace, kuma hanyoyinsu ba su da kyau; babu wani mai aikata abu mai kyau.

  5. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil ta Dawuda. Sa’ad da Zifawa suka tafi wurin Shawulu suka ce, “Ba Dawuda ba ne yake ɓuya a cikinmu?” Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka; ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka.

  6. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil ta Dawuda. Ka ji addu’ata, ya Allah, kada ka ƙyale roƙona;

  7. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da murya “Kurciya a Itatuwan Oak Mai Nisa.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da Filistiyawa suka kama shi a birnin Gat. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, gama mutane sun tasar mini da zafi; dukan yini suna matsa harinsu.

  8. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da ya gudu daga Shawulu zuwa cikin kogo. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai, gama a gare ka raina yake samun mafaka. Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka sai masifar ta wuce.

  9. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Ku masu mulki tabbatacce kuna magana daidai? Kuna yin shari’a daidai a cikin mutane?

  10. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da Shawulu ya aiki mutane su yi tsaron gidan Dawuda don yă kashe shi. Ka cece ni daga abokan gābana, ya Allah; ka tsare ni daga waɗanda suka tayar mini.

  11. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin Alkawari.” Wani miktam ta Dawuda. Don koyarwa. Sa’ad da ya yaƙi Aram-Naharayim da Aram-Zoba, da kuma sa’ad da Yowab ya dawo ya bugi mutanen Edom dubu goma sha biyu a Kwarin Gishiri. Ka ki mu, ya Allah, ka kuma fashe kāriyarmu; ka yi fushi da mu, yanzu ka mai da mu!

  12. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda. Ka ji kukata, ya Allah; ka saurari addu’ata.

  13. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zaburar Dawuda. Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai; cetona na zuwa daga gare shi.

  14. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da yake a hamadar Yahuda. Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa.

  15. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ka ji ni, ya Allah, yayinda nake faɗin abin da yake damuna; ka tsare raina daga barazanan abokin gāba.

  16. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Wata waƙa. Yabo ya dace da kai, ya Allah, a Sihiyona; a gare ka za mu cika alkawuranmu

  17. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura. Waƙa. Bari Allah yă tashi, bari a watsar da abokan gābansa; bari maƙiyansa su gudu a gabansa.

  18. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Lilin.” Ta Dawuda. Ka cece ni, ya Allah, gama ruwa ya kai wuyata

  19. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Roƙo. Ka hanzarta, ya Allah, ka cece ni; Ya Ubangiji, zo da sauri ka taimake ni.

  20. Wannan ya kammala addu’o’in Dawuda ɗan Yesse.

  21. Ya zaɓi Dawuda bawansa ya kuma ɗauke shi daga ɗakin tumaki;

  22. Addu’ar Dawuda. Ka ji, ya Ubangiji, ka kuma amsa mini, gama ni matalauci ne mai bukata kuma.

  23. Ka ce, “Na yi alkawari da zaɓaɓɓena, na rantse wa Dawuda bawana,

  24. Na sami Dawuda bawana; da mai na mai tsarki na shafe shi.

  25. Sau ɗaya ba ƙari, na rantse da tsarkina, ba kuwa zan yi ƙarya wa Dawuda ba,