Tsallake zuwa abun ciki

David

968 ayoyi · 40 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci David

Tace bisa littafi
  1. Amma yanzu na zaɓi Urushalima domin Sunana yă kasance a can, na kuma zaɓi Dawuda yă yi mulkin mutanena Isra’ila.’

  2. “Mahaifina Dawuda ya yi niyya a zuciyarsa yă gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.

  3. Amma Ubangiji ya ce wa mahaifina Dawuda, ‘Domin yana a zuciyarka ka gina haikali domin Sunana, ka yi daidai da ka kasance da wannan a zuciyarka.

  4. “Ubangiji ya kiyaye alkawarin da ya yi. Na gāje Dawuda mahaifina yanzu kuwa na zauna a kan kujerar sarautar Isra’ila, kamar dai yadda Ubangiji ya alkawarta, na kuma gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.

  5. Ka kiyaye alkawarinka ga bawanka Dawuda mahaifina; da bakinka ka yi alkawari kuma da hannunka ka cika shi, yadda yake a yau.

  6. “Yanzu fa Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka kiyaye wa bawanka Dawuda mahaifina alkawuran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka kāsa kasance da mutumin da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza za su kula cikin dukan abin da suke yi su yi tafiya a gabana bisa ga dokata, kamar yadda ka yi.’

  7. Yanzu kuwa, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bari maganarka da ka yi alkawarta wa bawanka Dawuda yă cika.

  8. Ya Ubangiji Allah, kada ka ƙyale shafaffenka.

  9. Firistoci suka ɗauki matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a matsayinsu riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Ubangiji, waɗanda Sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji. An yi amfani da su sa’ad da ake godiya, ana kuma cewa, “Ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Kurkusa da Lawiyawa, firistoci suka busa ƙahoninsu, dukan Isra’ila kuwa suna a tsaye.

  10. A rana ta ashirin da uku na watan bakwai sai ya sallami mutane su tafi gidajensu da farin ciki da kuma murna a zuciya saboda abubuwa masu kyau da Ubangiji ya yi domin Dawuda da Solomon da kuma domin mutanensa Isra’ila.

  11. “Game da kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka kuma yi dukan abin da na umarta, ka kiyaye ƙa’idodina da dokokina,

  12. zan kafa kujerar sarautarka, yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani mutumin da zai yi mulki a bisa Isra’ila ba.’

  13. Solomon ya kawo ’yar Fir’auna daga Birnin Dawuda zuwa fadan da ya gina mata, gama ya ce, “Matata ba za tă zauna a fadan Dawuda sarkin Isra’ila ba, domin wuraren da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga masu tsarki ne.”

  14. Bisa ga farillar mahaifinsa Dawuda, ya naɗa ɓangarori na firistoci don ayyukansu da Lawiyawa don su jagoranci yabo su kuma taimaki firistoci bisa ga bukace-bukacen kowace rana. Ya kuma naɗa matsara ƙofofi ɓangarori, ɓangarori don ƙofofi dabam-dabam domin abin da Dawuda mutumin Allah ya umarta ke nan.

  15. Sa’an nan ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi cikin birnin Dawuda mahaifinsa. Rehobowam ɗansa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.

  16. Sa’ad da Isra’ila suka ga sarki ya ƙi yă saurare su, sai suka amsa wa sarki, suka ce, “Wanda rabo muke da shi a wurin Dawuda, wanda sashe muke da shi daga ɗan Yesse? Kowa yă koma tentinsa, ya Isra’ila! Ka lura da gidanka, ya Dawuda!” Saboda haka dukan Isra’ilawa suka tafi gida.

  17. Ta haka Isra’ila ya kasance cikin tawaye a kan gidan Dawuda har yă zuwa wannan rana.

  18. Suka ƙarfafa mulkin Yahuda suka kuma goyi bayan Rehobowam ɗan Solomon shekaru uku, suna tafiya a hanyoyin Dawuda da Solomon a wannan lokaci.

  19. Rehobowam ya auri Mahalat, ’yar Yerimot ɗan Dawuda wadda Abihayil ’yar Eliyab ɗan Yesse ta haifa.

  20. Rehobowam ya huta da kakanninsa aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Abiya ɗansa kuma ya gāje shi a matsayin sarki.

  21. Ba ku san cewa Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ba da sarautar Isra’ila ga Dawuda da zuriyarsa har abada ta wurin alkawarin gishiri ba?

  22. Duk da haka Yerobowam ɗan Nebat, ma’aikacin Solomon ɗan Dawuda, ya tayar wa maigidansa,

  23. “Yanzu kuna shirin yin tsayayya da mulkin Ubangiji, wanda yake a hannuwan zuriyar Dawuda. Tabbatacce ku ƙasaitacciyar mayaƙa ne kuma kuna tare da ku maruƙan zinariyar da Yerobowam ya yi domin su zama allolinku.

  24. Abiya kuwa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Asa ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki, a zamaninsa kuma ƙasar ta zauna lafiya na shekara goma.

  25. Suka binne shi a kabarin da ya fafe wa kansa a Birnin Dawuda. Suka sa shi a makara wadda aka rufe da kayan yaji da kuma turare dabam-dabam da aka niƙa, suka kuma ƙuna babbar wuta don girmama shi.