Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Waiting Upon God

61 ayoyi · 68 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji.

  2. Yana da mata biyu, ɗaya sunanta Hannatu, ɗayan kuwa ana kiranta Feninna. Ita Feninna tana da ’ya’ya, amma Hannatu ba ta da ’ya’ya.

  3. Ba wanda yake sa bege a gare ka da zai taɓa shan kunya, amma za su sha kunya su da suke tayarwa babu dalili.

  4. ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini, gama kai ne Allah Mai cetona, kuma begena yana a kanka dukan yini.

  5. Bari mutunci da adalci su tsare ni, domin begena yana a kanka.

  6. Ka dogara ga Ubangiji, ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya ka kuma dogara ga Ubangiji.

  7. Muna jiran Ubangiji da bege; shi ne taimakonmu da garkuwarmu.

  8. Ka natsu a gaban Ubangiji ka kuma jira da haƙuri gare shi; kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu, sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.

  9. Gama za a datse mugayen mutane, amma waɗanda suke sa zuciya ga Ubangiji za su gāji ƙasar.

  10. “Amma yanzu, ya Ubangiji, me zan nema? Begena yana a gare ka.

  11. Ka cece ni daga dukan laifofina; kada ka sa in zama abin dariya ga wawaye.

  12. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Na jira da haƙuri ga Ubangiji; ya juya wurina ya kuma ji kukata.

  13. Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi; a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau. Zan yabe ka a gaban tsarkakanka.

  14. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da Shawulu ya aiki mutane su yi tsaron gidan Dawuda don yă kashe shi. Ka cece ni daga abokan gābana, ya Allah; ka tsare ni daga waɗanda suka tayar mini.

  15. Ka kuɓutar da ni daga masu aikata mugunta ka kuma cece ni daga masu kisa.

  16. Duba yadda suka kwanta suna jirana! Mugaye suna ƙulle-ƙullen gāba da ni ba saboda wani dalili ko na yi wa wani zunubi ba, ya Ubangiji.

  17. Ban yi wani laifi ba, duk da haka suna a shirye su fāɗa mini. Tashi ka taimake ni; dubi halin da nake ciki!

  18. Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, ka tashi ka hukunta dukan al’ummai; kada ka nuna jinƙai ga mugaye maciya amana. Sela

  19. Sukan dawo da yamma, suna wage haƙora kamar karnuka, suna yawo a birni.

  20. Dubi abin da suke tofawa daga bakunansu, suna tofar da takuba daga leɓunansu, suna cewa, “Wa zai ji mu?”

  21. Amma kai, ya Ubangiji, kakan yi musu dariya; kana yi wa dukan waɗannan al’ummai ba’a.

  22. Ya ƙarfina, na dogara gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata,

  23. Allah mai ƙaunata. Allah zai sha gabana zai kuma sa in yi dariya a kan waɗanda suke magana marar kyau a kaina.

  24. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zaburar Dawuda. Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai; cetona na zuwa daga gare shi.

  25. Shi kaɗai ne dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.