Skip to content

Joseph

6 ayoyi

Ayoyin da suka ambaci Joseph

  1. Da yamma ta yi, sai ga wani mutum mai arziki daga Arimateya, sunansa Yusuf, wanda shi da kansa almajirin Yesu ne.

  2. Yusuf ya ɗauki jikin ya nannaɗe shi da zanen lilin mai tsabta.

  3. Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.

  4. Da ya ji ta bakin jarumin cewa haka ne, sai ya ba wa Yusuf jikin.

  5. Akwai wani mutum mai suna Yusuf, ɗan Majalisa, wanda shi nagari ne, mai adalci,

  6. Bayan haka, Yusuf mutumin Arimateya ya roƙi Bilatus a ba shi jikin Yesu. Yusuf dai almajirin Yesu ne, amma a ɓoye domin yana tsoron Yahudawa. Da izinin Bilatus, ya zo ya ɗauki jikin.