Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tribute: From conquered nations

24 ayoyi · 24 fannoni

Ayoyi game da From conquered nations

  1. Ba su kori Kan’aniyawan da suke zama a Gezer ba, don haka Kan’aniyawa suna zama tare da mutanen Efraim har wa yau; amma Kan’aniyawa suka zama masu yin aikin dole.

  2. Haka kuma Zebulun bai kori Kan’aniyawa da suke zaune a Kitron da Nahalol, waɗanda suka rage a cikinsu ba; sai dai sun sa su aikin gandu.

  3. Haka Asher ma bai kori waɗanda suke zama a Akko ko Sidon ko Ahlab ko Akzib ko Helba ko Afik ko kuma Rehob ba,

  4. kuma saboda wannan ne mutanen Asher suke zaune cikin mazaunan ƙasar Kan’aniyawa.

  5. Haka kuma Naftali bai kori waɗanda suke zaune a Bet-Shemesh ko Bet-Anat; amma mutanen Naftali su ma suna zama a ciki Kan’aniyawa mazaunan ƙasar, waɗanda suke zaune a Bet-Shemesh da Bet-Anat kuwa suka zama masu yi musu aikin gandu.

  6. Sai Ful sarkin Assuriya ya kai wa ƙasar hari, Menahem kuwa ya ba shi talenti dubu na azurfa don yă sami goyon bayansa, yă kuma ƙarfafa kahuwa mulkin.

  7. Yehohiyakim ya riƙa biyan Fir’auna Neko azurfa da zinariyar da ya umarta. Don yă yi haka sai ya riƙa karɓar azurfa da zinariya daga mutanen ƙasar, kowa bisa ga ƙarfinsa.

  8. Bayan Yesu da almajiransa suka isa Kafarnahum, sai masu karɓan harajin rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku ba ya biyan harajin haikali ne?”

  9. Ya amsa ya ce “I, yana biya.” Da Bitrus ya shiga gida, Yesu ne ya fara magana. Ya ce masa, “Me ka gani, Siman? Daga wurin wane ne sarakunan duniya suke karɓar kuɗin shiga da kuma haraji, daga wurin ’ya’yansu ne ko kuwa daga wurin waɗansu?”

  10. Bitrus ya amsa ya ce, “Daga wurin waɗansu.” Yesu ya ce masa, “Wato, an ɗauke wa ’ya’yan ke nan.

  11. Amma don kada mu ɓata musu rai, ka je tafki ka jefa ƙugiyarka. Ka ɗauki kifin da ka fara kama; ka buɗe bakinsa, za ka sami shekel guda. Ka kawo ka ba su, harajina da naka ke nan.”

  12. Sai Farisiyawa suka yi waje, suka ƙulla yadda za su yi masa tarko cikin maganarsa.

  13. Suka aiki almajiransu tare da mutanen Hiridus wurinsa. Suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci, kuma kana koyar da maganar Allah bisa gaskiya. Mutane ba sa ɗaukan hankalinka, domin ba ka kula ko su wane ne ba.

  14. To, ka gaya mana, a ra’ayinka? Ya dace a biya Kaisar haraji ko a’a?”

  15. Amma Yesu da yake ya san mugun nufinsu, sai ya ce, “Ku munafukai, don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko?

  16. Ku nuna mini kuɗin da ake biyan haraji da shi.” Sai suka kawo masa dinari,

  17. sai ya tambaye su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne?”

  18. Suka amsa, “Na Kaisar ne.” Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”

  19. Da suka ji haka, sai suka yi mamaki. Saboda haka suka ƙyale shi, suka yi tafiyarsu.

  20. A waɗancan kwanaki, Kaisar Augustus ya ba da doka cewa ya kamata a yi ƙidaya a dukan masarautar Roma.

  21. (Wannan ce ƙidaya ta fari da aka yi a lokacin da Kwiriniyus yake gwamnar Suriya.)

  22. Sai kowa ya koma garinsa don a rubuta shi.

  23. Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne.

  24. Ya tafi can don a rubuta shi tare da Maryamu, wadda aka yi masa alkawari zai aura, tana kuwa da ciki.