Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tribute: Christ showed to the Pharisees and Herodians the propriety of paying

13 ayoyi · 24 fannoni

Ayoyi game da Christ showed to the Pharisees and Herodians the propriety of paying

  1. Sai Farisiyawa suka yi waje, suka ƙulla yadda za su yi masa tarko cikin maganarsa.

  2. Suka aiki almajiransu tare da mutanen Hiridus wurinsa. Suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci, kuma kana koyar da maganar Allah bisa gaskiya. Mutane ba sa ɗaukan hankalinka, domin ba ka kula ko su wane ne ba.

  3. To, ka gaya mana, a ra’ayinka? Ya dace a biya Kaisar haraji ko a’a?”

  4. Amma Yesu da yake ya san mugun nufinsu, sai ya ce, “Ku munafukai, don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko?

  5. Ku nuna mini kuɗin da ake biyan haraji da shi.” Sai suka kawo masa dinari,

  6. sai ya tambaye su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne?”

  7. Suka amsa, “Na Kaisar ne.” Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”

  8. Da suka ji haka, sai suka yi mamaki. Saboda haka suka ƙyale shi, suka yi tafiyarsu.

  9. Daga baya, sai suka tura waɗansu Farisiyawa da mutanen Hiridus zuwa wurin Yesu, domin su sa masa tarko a cikin maganarsa.

  10. Suka zo wurinsa suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci. Ba ka bin ra’ayin mutane, don ba ka nuna bambanci. Amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya. Daidai ne a biya wa Kaisar haraji, ko babu?

  11. Mu biya ko kada mu biya?” Amma Yesu ya san munafuncinsu, sai ya yi tambaya ya ce, “Don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? Ku kawo mini dinari in ga.”

  12. Suka kawo masa kuɗin, sai ya tambaye, su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne wannan?” Suka ce, “Na Kaisar.”

  13. Sai Yesu ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku ba wa Allah kuma abin da yake na Allah.” Suka yi mamakinsa ƙwarai.