Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Wisdom of God

61 ayoyi · 36 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji ya ce, “Tabbatacce na ga azabar mutanena a Masar. Na ji su suna kuka saboda matsin da shugabannin gandunsu suke musu, na kuma damu da wahalarsu.

  2. Ubangiji Allahnku ya albarkace ku cikin dukan aikin hannuwanku. Ya kiyaye ku cikin tafiyarku a duk fāɗin hamada. Waɗannan shekaru arba’in Ubangiji Allahnku ya kasance tare da ku, ba kuwa kun rasa wani abu ba.

  3. “Ka daina maganganu na girman kai ka kuma daina faɗin kalmomin ɗaga kai; gama Ubangiji Allah ne masani daga gare shi kuma ana auna ayyuka.

  4. “Me kuma Dawuda zai ce maka? Gama ka san bawanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka.

  5. “Kai kuma ɗana Solomon, ka san Allah na mahaifinka, ka kuma yi masa hidima da dukan zuciya da kuma yardar rai, gama Ubangiji yana binciken zuciya, yana kuma gane dukan aniyar tunani. In ka neme shi, za ka same shi; amma in ka yashe shi, zai ƙi ka har abada.

  6. Kai kuma Ezra, bisa ga hikimar da Allah ya ba ka, sai ka zaɓi mahukunta da alƙalai waɗanda za su zama masu yanke hukunci ga dukan mutanen Kewayen Kogin Yuferites, duk waɗanda suka san dokokin Allahnka, ka kuma koya wa duk waɗanda ba su san dokokin ba.

  7. Ka aika da alamu masu banmamaki da al’ajabai a kan Fir’auna, a kan dukan shugabanninsa da kuma a kan dukan mutanen ƙasarsa, gama ka ga irin danniyar da suka yi wa mutanenka. Ka samo wa kanka suna, wadda ta dawwama har yă zuwa yau.

  8. Hikimarsa tana da zurfi, ikonsa yana da yawa. Wane ne ya taɓa yin faɗa da shi har ya yi nasara?

  9. Ba shakka yana iya gane mutanen da suke marasa gaskiya; kuma in ya ga abin da yake mugu, ba ya kula ne?

  10. “Wani zai iya koya wa Allah ilimi tun da yana shari’anta har da waɗanda suke manya masu iko?

  11. Amma ya san hanyar da nake bi; sa’ad da ya gwada ni zan fito kamar zinariya.

  12. Gama yana ganin iyakar duniya kuma yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sama.

  13. “Idanunsa suna kan al’amuran mutane; yana ganin tafiyarsu duka.

  14. Abin da zan gaya maka ba ƙarya ba ne; mai cikakken sani yana tare da kai.

  15. “Allah mai iko ne, amma ba ya rena mutane; shi mai girma ne cikin manufarsa.

  16. Ko ka san yadda gizagizai suke tsayawa cik a sararin sama, waɗannan abubuwa al’ajabi na mai cikakken sani.

  17. Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa, amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.

  18. da Allah bai gane ba, da yake ya san asiran zuciya?

  19. Suna cewa, “Yaya Allah zai sani? Mafi Ɗaukaka yana da sani ne?”

  20. gama ya san yadda aka yi mu, ya tuna cewa mu ƙura ne.

  21. Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji! Cikin hikima ka yi su duka; duniya ta cika da halittunka.

  22. Wanda ta wurin ganewarsa ya yi sammai, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  23. Ka san sa’ad da na zauna da sa’ad da na tashi; ka san tunanina daga nesa.

  24. Ka san fitata da kuma kwanciyata; ka saba da dukan hanyoyina.

  25. Kafin in yi magana da harshena ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji.