Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Tribe Of Naphtali

48 ayoyi · 26 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Iyakar kuma ta juya yamma ta cikin Aznot-Tabo ta ɓulla a Hukkok. Ta taɓa Zebulun a kudu, Asher a yamma, da kuma Urdun a gabas.

  2. Biranen da suke da katanga su ne Ziddim, Zer, Hammat, Rakkat, Kinneret,

  3. Adama, Rama, Hazor,

  4. Kedesh, Edireyi, En Hazor,

  5. Yiron, Migdal El, Horem, Bet-Anat da Bet-Shemesh. Garuruwa goma sha tara ke nan da ƙauyukansu.

  6. Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon da kabilar Naftali ta samu, bisa ga iyalansu.

  7. Haka kuma Naftali bai kori waɗanda suke zaune a Bet-Shemesh ko Bet-Anat; amma mutanen Naftali su ma suna zama a ciki Kan’aniyawa mazaunan ƙasar, waɗanda suke zaune a Bet-Shemesh da Bet-Anat kuwa suka zama masu yi musu aikin gandu.

  8. Sai ta aika a kira mata Barak ɗan Abinowam daga Kedesh a Naftali, ta ce masa, “Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce ka, ‘Je ka, ka ɗauki mutane Naftali da na Zebulun dubu goma tare da kai, ka yi jagoransu zuwa Dutse Tabor.

  9. a can Barak ya kira Zebulun da Naftali. Mutum dubu goma suka kuma bi shi, Debora kuma tana tare da shi.

  10. Mutanen Zebulun sun kasai da rayukansu; haka ma Naftali a bakin dāgā.

  11. Aka kira dukan Isra’ilawa daga Naftali, Asher da dukan Manasse, suka kuwa fatattaki Midiyawa.

  12. Ahimawaz, shi ne a Naftali (ya auri Basemat ’yar Solomon);

  13. wanda mahaifiyarsa gwauruwa ce daga kabilar Naftali, wanda kuma mahaifinsa mutumin Taya ne, shi Huram, gwani ne a aikin tagulla. Huram gwani ne sosai kuma ya saba da yin kowane irin aikin tagulla. Sai ya zo wurin Sarki Solomon ya kuma yi dukan aikin da aka sa shi.

  14. Ben-Hadad ya yarda da maganar Sarki Asa, ya kuma aika shugabannin sojojin mayaƙansa ya yi yaƙi da garuruwan Isra’ila. Ya kame Iyon, Dan, Abel-Bet-Ma’aka da dukan Kinneret, haɗe da Naftali.

  15. A zamanin Feka sarkin Isra’ila, Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya zo ya kama Iyon, Abel-Bet-Ma’aka, Yanowa da Kedesh da kuma Hazor. Ya kame Gileyad da Galili, haɗe da dukan ƙasar Naftali, ya kuma kwashi mutanen zuwa Assuriya.

  16. mutanen Naftali su 1,000 shugabanni, tare da mutane 37,000 masu riƙe garkuwa da masu;

  17. bisa mutanen Zebulun shi ne, Ishmahiya ɗan Obadiya; bisa mutanen Naftali shi ne, Yerimot ɗan Azriyel;

  18. Ya yi haka cikin garuruwan Manasse, Efraim da Simeyon, har zuwa Naftali, da kuma cikin kangwayen kewayensu,

  19. Duk da haka, babu sauran baƙin ciki ga waɗanda suke shan azaba. Dā ya ƙasƙantar da ƙasar kabilan Zebulun da ƙasar Naftali, amma nan gaba zai girmama Galili na Al’ummai, ta hanyar teku wadda take ta Urdun.

  20. Mutanen da suke tafiya cikin duhu sun ga babban haske; a kan waɗanda suke zama a ƙasar inuwar mutuwa haske ya haskaka.

  21. Ya bar Nazaret, ya je ya zauna a Kafarnahum, wadda take a bakin tafki wajen Zebulun da Naftali

  22. don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa,

  23. “Ƙasar Zebulun da ƙasar Naftali, da kuke a hanyar zuwa tekun Galili, a ƙetaren Urdun, wannan yankin Galili ta Al’ummai,