Skip to content

Kedesh

9 verses

33.1100, 35.5300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Kedesh

  1. sarkin Kedesh, ɗaya sarkin Yokneyam a Karmel, ɗaya

  2. Kedesh, Edireyi, En Hazor,

  3. Saboda haka suka keɓe Kedesh a Galili a ƙasar kan tudu ta Naftali, Shekem a ƙasar kan tudu ta Efraim, da Kiriyat Arba (wato, Hebron) a ƙasar kan tudu ta Yahuda.

  4. daga kabilar Naftali kuma aka ba su, Kedesh a cikin Galili (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), Hammon-Dor da kuma Kartan, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa uku ke nan.

  5. Debora ta ce, “To, shi ke nan, zan tafi tare da kai. Amma saboda yadda ka ɗauki wannan batun, darajar ba za tă zama taka ba, gama Ubangiji zai ba da Sisera a hannun mace.” Saboda haka Debora ta tafi tare da Barak zuwa Kedesh,

  6. a can Barak ya kira Zebulun da Naftali. Mutum dubu goma suka kuma bi shi, Debora kuma tana tare da shi.

  7. To, Heber Bakene ya riga ya bar Keniyawa, zuriyar Hobab, ɗan’uwan matar Musa, ya kafa tentinsa wajen babban itace a Za’anannim kusa da Kedesh.

  8. A zamanin Feka sarkin Isra’ila, Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya zo ya kama Iyon, Abel-Bet-Ma’aka, Yanowa da Kedesh da kuma Hazor. Ya kame Gileyad da Galili, haɗe da dukan ƙasar Naftali, ya kuma kwashi mutanen zuwa Assuriya.

  9. daga kabilar Naftali kuwa suka sami Kedesh a Galili, Hammon da Kiriyatayim, tare da wuraren kiwonsu.