Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Tribe Of Naphtali: Bounds of their inheritance
Ayoyi game da Bounds of their inheritance
Ƙuri’a ta shida ta fāɗa a kan kabilar Naftali, bisa ga iyalansu.
Iyakarsu ta kama daga Helef, daga babban itacen Mamre nan da yake a Za’anannim, ta wuce Adami Nekeb da Yabneyel zuwa Lakkum, ta kuma ƙarasa a Urdun.
Iyakar kuma ta juya yamma ta cikin Aznot-Tabo ta ɓulla a Hukkok. Ta taɓa Zebulun a kudu, Asher a yamma, da kuma Urdun a gabas.
Biranen da suke da katanga su ne Ziddim, Zer, Hammat, Rakkat, Kinneret,
Adama, Rama, Hazor,
Kedesh, Edireyi, En Hazor,
Yiron, Migdal El, Horem, Bet-Anat da Bet-Shemesh. Garuruwa goma sha tara ke nan da ƙauyukansu.
Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne rabon da kabilar Naftali ta samu, bisa ga iyalansu.