Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Sun: (Darkened,) of severe calamities

5 ayoyi · 45 fannoni

Ayoyi game da (Darkened,) of severe calamities

  1. Sa’ad da na shafe ka, zan rufe sammai in duhunta taurarinsu; zan rufe rana da girgije, wata kuwa ba zai ba da haskensa ba.

  2. A gabansu duniya takan girgiza, sararin sama kuma yakan jijjigu, rana da wata su yi duhu, taurari kuma ba sa ba da haske.

  3. Rana za tă duhunta wata kuma yă zama jini kafin isowar babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji.

  4. “Nan da nan bayan tsabar wahalan nan “ ‘sai a duhunta rana, wata kuma ba zai ba da haskensa ba; taurari kuma za su fāffāɗi daga sararin sama, za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’

  5. Da ya buɗe Abis ɗin, sai hayaƙi ya taso daga cikin kamar hayaƙin matoya mai girma. Hayaƙin nan daga Abis ya duhunta rana da sararin sama.