Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Sabbath

85 ayoyi · 63 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A ranar Asabbaci na biye kusan dukan birnin suka taru don su ji maganar Ubangiji.

  2. Gama Musa ya yi wa’azi a kowace birni tun zamanin dā, ana kuma karanta shi a majami’u kowane Asabbaci.”

  3. A Asabbaci, muka fita ƙofar birnin zuwa bakin kogi, inda muke tsammani za mu sami wurin yin addu’a. Muka zauna muka fara yin wa matan da suka taru a can magana.

  4. Kamar yadda ya saba, Bulus ya shiga majami’ar, ranakun Asabbaci uku ya yi ta yin muhawwara da su daga cikin Nassosi,

  5. Kowace Asabbaci kuwa yakan yi muhawwara a majami’a, yana ƙoƙari yă rinjayi Yahudawa da Hellenawa.

  6. A ranar farko ta mako muka taru wuri ɗaya don gutsuttsura burodi. Bulus ya yi wa mutane magana, don yana niyyar tashi kashegari, sai ya yi ta yin magana har tsakar dare.

  7. A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe ’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba.

  8. Gama a wani wuri ya yi magana a kan rana ta bakwai cikin waɗannan kalmomi, “A rana ta bakwai kuwa Allah ya huta daga dukan aikinsa.”

  9. Har yanzu, akwai wani hutun Asabbacin da ya rage domin mutanen Allah;

  10. A Ranar Ubangiji ina cikin Ruhu, sai na ji a bayana wata babbar murya kamar ƙaho,