Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Sabbath: Punishment of those who profane
Ayoyi game da Punishment of those who profane
“ ‘Ku kiyaye Asabbaci, domin yă zama mai tsarki a gare ku. Duk wanda ya ƙazantar da shi, za a kashe shi; duk wanda ya yi wani aiki a ranar, za a ware shi daga mutane.
Kwana shida, za a yi aiki, amma a rana ta bakwai, Asabbaci ne na hutu, mai tsarki ga Ubangiji. Duk wanda ya yi wani aiki a Asabbaci, za a kashe shi.
Yayinda Isra’ilawa suke ciki hamada, sai aka sami wani mutum yana tattara itace a ranar Asabbaci.
Waɗanda suka gan shi, suka kawo shi wurin Musa da Haruna da dukan taro,
sai suka sa shi a gidan waƙafi don ba su riga sun san abin da za a yi da shi ba tukuna.
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Dole mutumin yă mutu. Dole dukan taron su jajjefe shi a bayan sansani.”
Saboda haka taron suka ɗauke shi zuwa bayan sansani, suka kuma jajjefe shi har ya mutu, yadda Ubangiji ya umarci Musa.