Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Sabbath: First day of the week kept as, by the church
Ayoyi game da First day of the week kept as, by the church
Bayan mako guda, har wa yau almajiransa suna cikin gidan, Toma kuwa yana tare da su. Ko da yake ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!”
A ranar farko ta mako muka taru wuri ɗaya don gutsuttsura burodi. Bulus ya yi wa mutane magana, don yana niyyar tashi kashegari, sai ya yi ta yin magana har tsakar dare.
A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe ’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba.