Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Sabbath: The seventh day observed as
Ayoyi game da The seventh day observed as
Kwana shida za ka yi dukan aikinka,
amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai.
Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.