Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Poor: Churches of Macedonia and Achaia

6 ayoyi · 92 fannoni

Ayoyi game da Churches of Macedonia and Achaia

  1. Gama Makidoniya da Akayya sun ji daɗin yin gudummawa domin matalautan da suke cikin tsarkakan da suke a Urushalima.

  2. To, ’yan’uwa, muna so ku san abin da alherin Allah ya ba wa ikkilisiyoyin Makidoniya.

  3. Gama sun sha wuya sosai saboda tsananin wahalar da suka shiga, har yawan farin cikinsu ya kai su ga yin alheri ta bayarwa ga waɗansu, ko da yake suna cikin tsananin talauci.

  4. Gama ina shaida cewa sun bayar daidai gwargwadon iyawarsu, har ma fiye da ƙarfinsu. Su kansu,

  5. sun roƙe mu sosai don su sami damar yin bayarwa a wannan hidima ga tsarkaka.

  6. Ba su yi yadda muka za tă ba, sai ma suka fara ba da kansu ga Ubangiji, sa’an nan sai suka ba da kansu gare mu bisa ga nufin Allah.