Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Poor: Oppress

8 ayoyi · 92 fannoni

Ayoyi game da Oppress

  1. Suna ture matalauta daga hanya suna kuma sa dole matalautan ƙasar su ɓoye.

  2. Kamar jakunan jeji a hamada, matalauta suna aikin neman abinci gonaki marasa amfani suna tanada abinci wa ’ya’yansu.

  3. Suna girbi a gonakin da ba nasu ba, suna yin kala a gonar inabi ta mugaye.

  4. Don ba su da tufafi, sukan kwana tsirara; ba su da wani abin da zai rufe su cikin sanyi.

  5. Sun jiƙe sharkaf da ruwan da yake kwararowa daga duwatsu, sun rungume duwatsu don rashin wurin fakewa.

  6. Ana ƙwace jinjiri mai shan mama; ana ƙwace ɗan yaron matalauci don biyan bashi.

  7. Don ba su da tufafi suna yawo tsirara; suna dakon dammunan hatsi amma duk da haka suna cikin shan yunwa.

  8. Yakan ci zalin matalauta da mabukata. Yakan yi fashi. Ba ya mayar da abin da aka jinginar masa. Ya dogara ga gumaka. Yana aikata ayyukan banƙyama.