Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Levites

255 ayoyi · 63 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. ta ashirin da huɗu a kan Romamti-Ezer, na goma sha biya a kan Yerimot, ’ya’yansa maza da danginsa 12.

  2. kashi ɗaya bisa ukunku a fadan sarki, kashi ɗaya bisa uku kuma, a Ƙofar Harsashi, sai kuma dukan sauran mutane su kasance a filayen haikalin Ubangiji.

  3. Babu wanda zai shiga haikalin Ubangiji sai firistoci da Lawiyawan da suke a aiki; za su iya shiga domin su tsarkaku ne, amma sauran mutane za su kiyaye abin da Ubangiji ya sa su yi.

  4. Lawiyawa za su tsaya kewaye da sarki, kowane mutum da makamansa a hannunsa. Duk wanda ya shiga haikali sai a kashe shi. Ku tsaya kusa da sarki a duk inda ya tafi.”

  5. Hezekiya ya ba da umarni a shirya ɗakunan ajiya a haikalin Ubangiji, aka kuwa yi haka.

  6. Sa’an nan cikin aminci suka kawo taimako, zakka da keɓaɓɓun kyautai. Konaniya, wani Balawe, shi ne ke lura da waɗannan abubuwa, kuma ɗan’uwansa Shimeyi shi ne na biye da shi.

  7. Yehiyel, Azaziya, Nahat, Asahel, Yerimot, Yozabad, Eliyel, Ismakiya, Mahat da Benahiya su ne shugabanni, mataimakan Konaniya da Shimeyi ɗan’uwansa, waɗanda sarki Hezekiya da Azariya babban shugaban haikalin Allah suka naɗa.

  8. Kore ɗan Imna Balawe, mai tsaron Ƙofar Gabas, shi ne yake lura da baikon yardan ran da aka yi wa Allah, don ya karkasa bayarwar da aka keɓe domin Ubangiji da hadayu mafi tsarki.

  9. Eden, Miniyamin, Yeshuwa, Shemahiya, Amariya da Shekaniya sun taimake shi da aminci a cikin garuruwan firistoci, suna ba da rabo wa ’yan’uwansu firistoci bisa ga sassansu, tsofaffi da yara.

  10. Bugu da ƙari, suka ba da rabo ga maza ’yan shekaru uku ko fiye waɗanda sunayensu suna a tarihin zuriya, dukan waɗanda ba za su iya shiga haikalin Ubangiji su yi ayyukansu na kullum ba, bisa ga nawayarsu da kuma sassansu.

  11. Suka kuma ba da rabo ga firistocin da aka rubuta ta iyalansu cikin tarihin zuriya, haka kuma ga Lawiyawa masu shekara ashirin ko fiye, bisa ga nawayarsu da kuma sassansu.

  12. Suka haɗa da dukan ƙanana ’ya’yansu, mata, da kuma ’ya’ya maza da ’ya’ya mata, al’umma gaba ɗaya da aka jera a waɗannan tarihin zuriya. Gama sun yi aminci cikin tsarkake kansu.

  13. Akwai mutane a garuruwa da yawa waɗanda aka sa don su rarraba wa ’ya’yan Haruna, firist, maza, waɗanda suke zaune a gonaki na ƙasar garuruwansu su ba kowane namijin da aka rubuta na Lawiyawa, rabonsa.

  14. A keɓewar katangar Urushalima, an nemi Lawiyawa daga inda suke zama aka kawo su Urushalima don su yi bikin miƙawa da farin ciki da waƙoƙin godiya da kuma kiɗin kuge, garaya da molo.

  15. Aka kuma tattara mawaƙa su ma daga yankin kewayen Urushalima, daga ƙauyukan Netofawa,

  16. daga Bet-Gilgal, da kuma daga wuraren Geba da Azmawet, gama mawaƙan sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Urushalima.

  17. Sa’ad da firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu da tsarki, sai suka tsarkake mutane, ƙofofi da kuma katanga.

  18. Sai na sa shugabannin Yahuda suka haura zuwa bisan katangar. Na kuma sa manyan ƙungiyoyi biyu na mawaƙa su miƙa godiya. Ɗaya ya haura zuwa bisan katangar zuwa dama, wajen Ƙofar Juji.

  19. Hoshahiya da rabin shugabannin Yahuda kuwa suka bi su,

  20. tare da Azariya, Ezra, Meshullam,

  21. Yahuda, Benyamin, Shemahiya, Irmiya,

  22. da waɗansu firistoci kuma da ƙahoni, da kuma Zakariya ɗan Yonatan, ɗan Shemahiya, ɗan Mattaniya, ɗan Mikahiya, ɗan Zakkur, ɗan Asaf,

  23. da ’yan’uwansa, Shemahiya, Azarel, Milalai, Gilalai, Ma’ai, Netanel, Yahuda da Hanani, tare da kayan kiɗi da Dawuda mutumin Allah ya umarta. Ezra malamin Doka ya jagoranci jerin gwanon.

  24. A Ƙofar Maɓuɓɓuga suka ci gaba kai tsaye suka haura matakalan Birnin Dawuda a kan hawa zuwa katangar suka wuce a bisa gidan Dawuda zuwa Ƙofar Ruwa wajen gabas.

  25. Ƙungiyar mawaƙa ta biyu suka yi jerin gwano a ɗaya gefen. Na bi su a bisan katangar, tare da rabin mutanen, muka wuce Hasumiya Tanderu zuwa Katanga Mai Faɗi,