Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Edomites: Governed by dukes

20 ayoyi · 62 fannoni

Ayoyi game da Governed by dukes

  1. Waɗannan su ne manya a cikin zuriyar Isuwa, ’Ya’ya Elifaz maza ɗan farin Isuwa, Shugabannin su ne; Teman, Omar, Zefo, Kenaz,

  2. Kora, Gatam da kuma Amalek. Waɗannan ne manya da suka fito daga dangin Elifaz a Edom; su ne jikokin Ada.

  3. ’Ya’yan Reyuwel maza, Shugabannin su ne; Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Reyuwel a Edom; su ne jikokin Basemat matar Isuwa.

  4. ’Ya’yan Oholibama maza matar Isuwa, Shugabannin su ne; Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Oholibama ’yar Ana matar Isuwa.

  5. Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza (wato, Edom), waɗannan ne manyansu.

  6. Waɗannan su ne ’ya’yan Seyir Bahore maza, waɗanda suke zaune a yankin, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana,

  7. Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, ’ya’yan Seyir, maza, a ƙasar Edom.

  8. ’Ya’yan Lotan maza su ne, Hori da Homam. Timna ’yar’uwar Lotan ce.

  9. ’Ya’yan Shobal maza su ne, Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam.

  10. ’Ya’yan Zibeyon maza su ne, Aiya da Ana. Wannan shi ne Ana wanda ya sami maɓulɓulan ruwan zafi a hamada yayinda yake kiwon jakuna na mahaifinsa Zibeyon.

  11. ’Ya’yan Ana su ne, Dishon da Oholibama ’yar Ana.

  12. ’Ya’yan Dishon maza su ne, Hemdan, Eshban, Itran da Keran.

  13. ’Ya’yan Ezer maza su ne, Bilhan, Za’aban da Akan.

  14. ’Ya’yan Dishan maza su ne, Uz da Aran.

  15. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana,

  16. Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, bisa ga ɓangarorinsu, a ƙasar Seyir.

  17. Waɗannan su ne manya da suka fito daga zuriyar Isuwa, bisa ga danginsu, bisa kuma ga kabilansu da yankunansu. Sunayensu su ne, Timna, Alwa, Yetet.

  18. Oholibama, Ela, Finon.

  19. Kenaz, Teman, Mibzar.

  20. Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom bisa ga mazauninsu cikin ƙasar da suka zauna. Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom.