Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Edomites: The king of Babylon an instrument of their punishment
Ayoyi game da The king of Babylon an instrument of their punishment
Sa’an nan ka aika da saƙo zuwa wurin sarakunan Edom, Mowab, Ammon, Taya da Sidon ta bakin jakadu waɗanda suka zo Urushalima wurin Zedekiya sarkin Yahuda.
Ka ba su saƙo wa iyayengijinsu su ce, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Ku faɗa wa iyayengijinku wannan.
Da ikon mai ƙarfi da kuma hannuna da na miƙa na yi duniya da mutanenta da kuma dabbobin da suke ciki, na ba da ita ga duk wanda na ga dama.
Yanzu zan ba da dukan ƙasashenku ga bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon; zan sa namun jeji ma su bauta masa.