Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Edomites: Revolted from Joram, king of Judah

6 ayoyi · 62 fannoni

Ayoyi game da Revolted from Joram, king of Judah

  1. A kwanakin Yoram, Edom ta yi wa Yahuda tawaye, ta naɗa wa kanta sarki.

  2. Saboda haka Yehoram ya tafi Zayir da dukan kekunan yaƙinsa. Sojojin Edom suka kewaye shi a can, amma da dare sai Yoram ya ɓarke ya gudu, sojojinsa kuma suka watse zuwa gidajensu.

  3. Har yă zuwa yau, Edom tana yi wa Yahuda tawaye. A lokaci ɗaya ne Libna ma ta yi tawaye.

  4. A zamanin Yehoram, Edom ya tayar wa Yahuda ya kuma naɗa sarkinsa.

  5. Saboda haka Yehoram ya tafi can tare da shugabannin sojojinsa da kuma dukan keken yaƙinsa. Mutanen Edom suka kewaye shi da shugabannin keken yaƙinsa, amma ya tashi ya fatattaki su da dare.

  6. Har yă zuwa yau Edom na tawaye a kan Yahuda. Libna ya yi tawaye a lokaci guda, domin Yehoram ya yashe Ubangiji Allah na kakanninsa.