Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Edomites: Utter desolation of their country

18 ayoyi · 62 fannoni

Ayoyi game da Utter desolation of their country

  1. Za a mai da rafuffukan Edom rami, ƙurarta za tă zama kibiritun farar wuta; ƙasarta za tă zama rami mai ƙuna!

  2. Ba za a kashe ta ba dare da rana; hayaƙinta za tă yi ta tashi har abada. Daga tsara zuwa tsara za tă zama kango; babu wani da zai ƙara wucewa ta wurin.

  3. Mujiyar hamada da mujiya mai kuka za su mallake ta; babban mujiya da hankaka za su yi sheƙa a can. Allah zai miƙe a kan Edom magwajin bala’i da ma’aunin kango.

  4. Sarakunanta ba za su kasance da wani abin da ake kira masarauta ba, dukan sarakunanta za su ɓace.

  5. Ƙayayuwa za su mamaye fadodinta ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za su cika kagaranta. Za tă zama mazaunin diloli da gida don mujiyoyi.

  6. Halittun hamada za su sadu da kuraye, awakin jeji za su yi ta kiran juna; a can halittun dare su ma za su huta su kuma nemi wurin hutu wa kansu.

  7. Mujiya za tă yi sheƙa a can ta zuba ƙwai; za tă ƙyanƙyashe su, ta kuma kula da ’ya’yanta a inuwar fikafikanta; a can kuma shirwa za su taru, kowa da abokinsa.

  8. Duba a cikin littafin Ubangiji ka kuma karanta. Babu wani a cikin waɗannan da ya ɓace, babu ko ɗaya da ba ta da abokiya. Gama bakinsa ne ya ba da umarni, Ruhunsa kuma zai tara su wuri ɗaya.

  9. Ya ba su rabonsu; hannunsa ya rarraba musu ta wurin awo. Za su mallake ta har abada su kuma zauna a can daga tsara zuwa tsara.

  10. Zan mai da Dutsen Seyir kango in kuma yanke dukan waɗanda suke shiga da fita a cikinka.

  11. Zan cika duwatsunka da matattu; waɗanda aka kashe da takobi za su fāɗi a kan tuddanka, da cikin kwarurukanka, da cikin dukan kwazazzabanka.

  12. Zan mai da kai kango har abada; ba za a zauna a cikin garuruwanka ba. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.

  13. “ ‘Domin kun ce, “Waɗannan al’ummai biyu da ƙasashe za su zama namu za mu kuma mallake su,” ko da yake Ni Ubangiji ina a can,

  14. saboda haka muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan sāka maka gwargwadon fushi da kuma kishin da ka nuna a ƙiyayyarsu da ka yi zan kuma sanar da kaina a cikinsu sa’ad da na hukunta ka.

  15. Sa’an nan za ka san cewa Ni Ubangiji na ji duk abubuwan banzan da ka faɗa a kan duwatsun Isra’ila. Ka ce, “An mai da su kango an kuma ba mu su mu cinye.”

  16. Ka yi fariya a kaina, ka kuma yi magana a kaina ba gaggautawa, na ji shi sarai.

  17. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa yayinda dukan duniya take farin ciki, zan mai da kai kango.

  18. Domin ka yi farin ciki sa’ad da gādon gidan Isra’ila ya zama kufai, haka zan yi da kai, ya Dutsen Seyir, kai da dukan Edom. Sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.’ ”