Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Tact

84 ayoyi · 11 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yowab ya rusuna har ƙasa don bangirma, ya kuma yi wa sarki kyakkyawar fata. Yowab ya ce, “Yau, bawanka ya sani ya sami tagomashi a gare ka, ranka yă daɗe sarki, gama sarki ya ji roƙon bawansa.”

  2. Sai wata mata mai hikima ta yi kira daga ciki birnin ta ce, “Ku saurara! Ku saurara! Ku gaya wa Yowab yă zo nan ina so in yi magana da shi.”

  3. Ya tafi wurinta, sai ta ce, “Kai ne Yowab?” Ya ce, “Ni ne”. Ta ce, “Ka ji abin da zan ce maka.” Ya ce, “Ina jinki.”

  4. Ta ci gaba ta ce, “A dā can, akan ce, ‘Sami amsarka a Abel,’ shi ke nan an gama.

  5. Mu ne masu salama da kuma amintattu na Isra’ila. Kana ƙoƙari ka hallaka birnin da yake uwa a Isra’ila. Don me kake so ka hallakar da gādon Ubangiji?”

  6. Yowab ya ce, “Allah yă sawwaƙe! Allah yă sawwaƙe in hallaka, ko in lalace gādon Ubangiji.

  7. Ba haka ba ne batun. Wani mai suna Sheba ɗan Bikri ne, daga ƙasar tudun Efraim, ya tayar wa sarki, yana gāba da Dawuda. Ki ba mu wannan mutum, zan kuwa janye daga birnin.” Matar ta ce wa Yowab, “Za a jefa maka kansa daga katanga.”

  8. Sa’an nan matar ta tafi wurin dukan mutane da shawararta mai hikima, sai suka datse kan Sheba ɗan Bikri suka jefa wa Yowab. Saboda haka sai ya busa ƙaho, mutanensa kuwa suka watse daga birnin, kowa ya koma gidansa. Yowab kuma ya koma wurin sarki a Urushalima.

  9. Sai sarki ya ce, “Kawo mini takobi.” Sai aka kawo takobi wa sarki.

  10. Ya ba da umarni ya ce, “Yanka yaron nan mai rai, gida biyu, kowacce ta ɗauki rabi.”

  11. Ainihin mamar ɗan da yake a raye ta cika da tausayi saboda ɗanta, sai ta ce wa sarki, “Ina roƙonka, ranka yă daɗe, kada ka kashe yaron! Ka ba ta kawai!” Amma ɗayan matar ta ce, “Kada a ba kowa daga cikinmu ɗan da rai, a ci gaba a raba shi!”

  12. Sai sarki ya zartar da hukuncinsa ya ce, “A ba da jariri mai ran ga mata ta fari. Kada a kashe shi; ita ce ainihin mahaifiyarsa.”

  13. Sa’ad da dukan Isra’ila suka ji hukuncin da sarki ya zartar, suka girmama sarki sosai, domin sun gane cewa Allah ya ba shi hikimar yin shari’ar adalci.

  14. Esta ba tă bayyana asalin al’ummarta da na iyalinta ba, domin Mordekai ya hana yin haka.

  15. Amsa da tattausar harshe kan kwantar da fushi, amma magana da kakkausan harshe kan kuta fushi.

  16. Ta wurin haƙuri akan rinjaye mai mulki, magana mai hankali kan karye ƙashi.

  17. Sai magatakardar birnin ya sa taron su yi shiru, sa’an nan ya ce, “Mutanen Afisa, ashe duk duniya ba tă san cewa birnin Afisa ce mai lura da haikalin Artemis mai girma da kuma siffarta da ya fāɗi daga sama ba?

  18. Saboda haka, da yake ba dama a yi mūsun wannan gaskiya, ya kamata ku natsu kada ku yi kome da garaje.

  19. Kun kawo mutanen nan a nan, gashi kuwa ba su yi fashin haikali ba, ba su kuwa saɓa wa alliyarmu ba.

  20. To, in haka ne, in Demetiriyus da abokan sana’arsa suna da wata magana game da wani ai, kotuna suna nan a buɗe, akwai kuma muƙaddasai. Suna iya kai ƙara.

  21. In kuma akwai wani abu har yanzu da kuke so ku kawo, dole a daidaita shi a majalisa.

  22. Yadda yake a yanzu, muna a hatsarin amsa zargin ta da hargitsi saboda abin da ya faru yau. Da yake ba za mu iya ba da dalilin da ya sa aka yi wannan hargitsi ba.”

  23. Bayan da ya faɗi haka, sai ya sallami taron.

  24. Da suka ji haka, sai suka yabi Allah. Sa’an nan suka ce wa Bulus, “Ka gani ɗan’uwa, yawan dubban Yahudawan da suka gaskata, kuma dukansu masu himma ne a wajen bin doka.

  25. An sanar da su cewa kana koya wa dukan Yahudawan da suke zama a cikin Al’ummai cewa su juye daga Musa, kana kuma faɗa musu kada su yi wa ’ya’yansu kaciya ko su yi rayuwa bisa ga al’adunmu.