Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sodom

91 ayoyi · 8 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Da suka fitar da su, sai ɗaya daga cikin mala’ikun ya ce, “Ku gudu domin ranku; kada ku duba baya, kada kuma ku tsaya ko’ina cikin kwarin! Ku gudu zuwa cikin duwatsu, don kada a hallaka ku!”

  2. Amma Lot ya ce musu, “A’a, ranka yă daɗe, ka yi haƙuri!

  3. Bawanku ya riga ya sami tagomashi daga gare ku, kun kuma nuna mini alheri mai yawa. Ba zan iya in gudu zuwa duwatsu ba, wannan masifa za tă same ni, zan kuma mutu.

  4. Ga ɗan gari can ya fi kusa inda zan gudu in fake. Bari in gudu zuwa can, in tsirar da raina.”

  5. Sai ya ce masa, “Na yarda da abin da ka ce, ba zan hallakar da garin da ka ambata ba.

  6. Gaggauta, ka gudu zuwa can, ba zan yi kome ba sai ka isa can.” (Domin haka ne ake kira garin Zowar.)

  7. A lokacin da Lot ya isa Zowar, rana ta hau.

  8. Sai Ubangiji ya yi ta zuba kibiritu a bisa Sodom da Gomorra daga sama.

  9. Haka ya hallakar da waɗannan birane da kuma kwarinsu gaba ɗaya, haɗe da dukan waɗanda suke zama a biranen, da kuma dukan shuke-shuke da suke cikin ƙasar.

  10. Amma matar Lot ta waiwaya baya, ta kuma zama ginshiƙin gishiri.

  11. Da sassafe kashegari, Ibrahim ya tashi ya koma wurin da dā ya tsaya a gaban Ubangiji.

  12. Ya duba ta wajen Sodom da Gomorra, da wajen dukan filayen ƙasar, sai ya ga hayaƙi baƙin ƙirin yana tashi daga ƙasar kamar hayaƙi daga matoya.

  13. Saboda haka sa’ad da Allah ya hallaka waɗannan biranen kwarin, ya tuna da Ibrahim, ya kuma fitar da Lot daga masifar da ta hallaka biranen da Lot ya zauna.

  14. Kada mutumin Isra’ila ko mutuniyar Isra’ila yă zama karuwar haikali.

  15. Ƙasar gaba ɗaya za tă zama gishiri mai ƙuna marar amfani da kuma kibiritu, babu shuki, babu abin da yake tsirowa, babu itatuwan da suke girma a cikinta. Za tă zama kamar yadda aka hallaka Sodom da Gomorra, Adma da Zeboyim, waɗanda Ubangiji ya hallaka cikin zafin fushinsa.

  16. Kuringarsu ta fito daga kuringar Sodom ne, daga gonakin Gomorra kuma. ’Ya’yan inabinsu dafi ne, nonnansu masu ɗaci ne.

  17. Ku saurari maganar Ubangiji, ku masu mulkin Sodom; ku kasa kunne ga dokar Allahnmu, ku mutanen Gomorra!

  18. Fuskokinsu shaidu ne a kansu; suna nuna zunubinsu a fili kamar yadda Sodom ya yi; ba sa ma ɓoye shi. Kaitonsu! Sun jawo wa kansu masifa.

  19. Babilon, kayan daraja na mulkoki, abin fariyar Babiloniyawa, Allah zai kaɓantar da ita kamar yadda ya yi da Sodom da Gomorra.

  20. A cikin annabawan Urushalima kuma na ga wani abin bantsoro. Suna zina suna kuma rayuwar ƙarya. Sun ƙarfafa hannuwa masu aikata mugunta, domin kada wani ya juya daga muguntarsa. Dukansu sun yi kama da Sodom a gare ni; mutanen Urushalima sun yi kama da Gomorra.”

  21. Kamar yadda aka tumɓuke Sodom da Gomorra, tare da garuruwan da suke maƙwabtaka da su,” in ji Ubangiji, “haka ba wanda zai zauna a can; ba wani da zai zauna a cikinta.

  22. Yadda Allah ya tumɓuke Sodom da Gomorra tare da maƙwabtan garuruwansu,” in ji Ubangiji “haka ma ba wanda zai zauna a can; ba wani da zai zauna a cikinta.

  23. Horon mutanena ya fi na Sodom girma, wadda aka hallaka farat ɗaya ba wani hannu da ya juya ya taimake ta.

  24. Babbar ’yar’uwarki mutuniyar Samariya ce, wadda take zaune da ’ya’yanta mata wajen arewa da ke; ƙanuwarki ita ce Sodom wadda take zaune kudu da ke tare da ’ya’yanta mata.

  25. Ba ki bi hanyoyinsu da abubuwansu na banƙyama kaɗai ba, sai ka ce wannan ya yi miki kaɗan, amma kin lalace fiye da su.