Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ships

79 ayoyi · 53 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kwana arba’in ambaliya ta yi ta saukowa a duniya, sa’ad da ruwa ya yi ta ƙaruwa sai ya yi ta ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can bisa duniya.

  2. Ruwa ya taso, ya ƙaru ƙwarai a duniya, jirgin kuma ya yi ta yawo a bisa ruwa.

  3. “Zebulun zai zauna a bakin teku, yă zama tasar jiragen ruwa; iyakarsa za tă nausa zuwa Sidon.

  4. Jiragen ruwa za su zo daga Kittim; za su murƙushe Asshur da Eber, amma su ma za a hallaka su.”

  5. Gileyad ya tsaya gaban Urdun. Kai kuma Dan, don me ka ka yi ta zama a wajen jiragen ruwa? Asher ya ci gaba da kasance a bakin teku ya kasance a wuraren zamansa.

  6. Sarki Solomon ya kuma gina jiragen ruwa a Eziyon Geber, wadda take kusa da Elot a Edom, a bakin Jan Teku.

  7. To, Yehoshafat ya gina jerin jiragen ruwan kasuwanci don su je Ofir saboda zinariya, amma ba su yi tafiya ba, gama sun farfashe a Eziyon Geber.

  8. Sai Hiram ya aika masa jiragen ruwan da masu tuƙinsu waɗanda suka san teku sosai. Ma’aikatan Hiram suka tafi da na Solomon zuwa Ofir suka dawo da talentin zinariya ɗari huɗu da hamsin wa Sarki Solomon.

  9. Sarki yana da jerin jiragen ruwa na kasuwanci waɗanda mutanen Hiram ne suke kula da su. Sau ɗaya kowace shekara uku sukan dawo ɗauke da zinariya, azurfa, hauren giwa, gogo da kuma birai.

  10. Suna wucewa kamar jirgin ruwan da aka yi da kyauro, kamar jahurma da ta kai wa namanta cafka.

  11. Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshish da iskar gabas ta wargaje.

  12. A can jiragen ruwa suna kai komo, kuma dodon ruwan da ka yi, yă yi wasa a can.

  13. Waɗansu suka yi tafiya a teku cikin jiragen ruwa; su ’yan kasuwa ne a manyan ruwaye.

  14. “Akwai abubuwa uku da suke ba ni mamaki, abubuwa huɗu da ba na iya fahimtarsu,

  15. yadda gaggafa take firiya a sararin sama, yadda maciji yake tafiya a kan dutse, yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku, da kuma sha’ani tsakanin namiji da ’ya mace.

  16. Ita kamar jirgin ’yan kasuwa ne tana kawo abincinta daga nesa.

  17. wadda ta aiko da jakadu ta teku cikin jiragen ruwan da aka yi da kyauro a bisa ruwa. Ku tafi, ku ’yan saƙo masu sauri, zuwa ga dogayen mutane masu sulɓin jiki, zuwa ga mutanen da ake jin tsoro a ko’ina, al’umma mai ƙarfin iko tana jawabin da ba a saba ji ba, mai ƙasar da koguna suka raba.

  18. Abin da Allah ya faɗa game da Taya. Ku yi kuka mai zafi, ya jiragen ruwan Tarshish! Gama an hallaka Taya aka kuma bar su babu gida ko tasha. Daga ƙasar Saifurus magana ta zo musu.

  19. Ku yi kuka mai zafi, ku jiragen ruwan Tarshish; an rurrushe kagararku!

  20. A can Ubangiji zai zama Mai Iko Duka namu. Zai zama kamar inda manyan koguna da rafuffuka suke. Matuƙan jirgin ruwa ba za su kai wurinsu ba, manyan jiragen ruwa ba za su yi zirga-zirga a kansu ba.

  21. Maɗaurinku sun kunce ƙarfafan itacen jirgin ba su da kāriya, fikafikan jirgin ba su buɗu ba. Ta haka za a raba yalwar ganima har ma guragu za su kwashe ganimar.

  22. Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, “Saboda ku zan aika Babilon in kawo dukan Babiloniyawa kamar masu gudun hijira, a cikin jiragen ruwa waɗanda suke taƙama da su.

  23. Babu shakka tsibirai suna dogara gare ni; jiragen Tarshish kuma su ne a gaba, suna kawo ’ya’yanki maza daga nesa, tare da azurfa da zinariya, domin su girmama Ubangiji Allahnki, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, gama ya cika ki da daraja.

  24. Sun yi dukan katakanki daga itatuwan fir daga Senir; sun kwaso itatuwan al’ul daga Lebanon don su yi miki jigon jirgin ruwa.

  25. Da oak daga Bashan suka yi sandunan tuƙan jirgin ruwa da itatuwan kasharina daga bakin tekun Saifurus suka yi daɓe jirgin ruwanki, suka kuma manne masa hauren giwa.