Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ships: Were often wrecked

7 ayoyi · 53 fannoni

Ayoyi game da Were often wrecked

  1. To, Yehoshafat ya gina jerin jiragen ruwan kasuwanci don su je Ofir saboda zinariya, amma ba su yi tafiya ba, gama sun farfashe a Eziyon Geber.

  2. Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshish da iskar gabas ta wargaje.

  3. Amma jirgin ruwan ya shiga yashi ya kafe. Kan jirgin ya shiga cikin yashin ya kāsa motsi, sai jirgin ya fara farfashewa ta baya saboda haukan raƙuman ruwa.

  4. Sojojin suka yi niyya su kakkashe ’yan kurkukun don hana waninsu yă yi iyo yă tsere.

  5. Amma jarumin ya so yă ceci ran Bulus, sai ya hana su aiwatar da niyyarsu. Ya kuma yi umarni duk waɗanda suka iya ruwa su fara fāɗawa zuwa gaci.

  6. Sauran kuma su bi katakai zuwa can ko kuma a kan tarkacen jirgin ruwan. Ta haka kowa ya kai bakin teku lafiya.

  7. Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni.