Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Self-Control

41 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma waɗansu ’yan iska suka ce, “Yaya wannan mutum zai iya cetonmu?” Suka rena shi suka ƙi su kawo masa kyautai. Amma Shawulu bai ce uffam ba.

  2. Bayan da Shawulu ya komo daga fafaran Filistiyawa, sai aka gaya masa cewa, “Dawuda yana can a Jejin En Gedi.”

  3. Saboda haka Shawulu ya zaɓi mutum dubu uku daga cikin dukan Isra’ila, suka fita neman Dawuda da mutanensa kusa da Duwatsun Awakin Jeji.

  4. Da Shawulu ya isa inda ake ajiye garken tumaki a bakin hanya inda akwai kogo, sai ya shiga ciki kogon don yă yi bayan gari. Dawuda da mutanensa kuwa suna can zaune a ƙurewar kogon.

  5. Mutanen Dawuda suka ce, wannan rana ce Ubangiji ya yi magana ya ce maka, “Zan ba da maƙiyinka a hannunka domin ka yi abin da ka ga dama da shi.” Sai Dawuda ya tashi a hankali ya je ya yanke shafin rigar Shawulu.

  6. Daga baya Dawuda ya damu domin ya yanke shafin rigar Shawulu.

  7. Ya ce wa mutanensa, “Ubangiji yă sawwaƙe in yi abu haka ga shugabana da Ubangiji ya shafe, ko in ɗaga hannuna in kashe shi, gama shi shafaffe ne na Ubangiji.”

  8. Da wannan magana Dawuda ya kwaɓi mutanensa, bai yarda su fāɗa wa Shawulu ba. Shawulu kuwa ya bar kogon ya yi tafiyarsa.

  9. Daga baya Dawuda ya fita daga kogon sai ya kira Shawulu ya ce, “Ranka yă daɗe, sarki!” Da Shawulu ya waiwaya, sai Dawuda ya rusuna da fuskarsa har ƙasa.

  10. Ya ce wa Shawulu, “Me ya sa kake saurari mutanen da suke cewa, ‘Dawuda ya dāge yă cuce ka’?

  11. Yau ka ga da idonka yadda Ubangiji ya bashe ka a hannuna a cikin kogon nan. Waɗansu sun ce mini in kashe ka, amma na bar ka, na ce, ‘Ba zan sa hannuna a kan shugabana ba, gama shi shafaffe ne na Ubangiji.’

  12. Babana, duba, ga shafin rigarka a hannuna, na yanke shafin rigarka amma ban kashe ka ba. Yanzu ka gane ka kuma sani cewa ba ni da laifin aikata kome ko tayarwa, ban yi maka laifi ba, amma kana farautar raina.

  13. Ubangiji zai shari’anta tsakanina da kai. Ubangiji zai sāka mini laifin da ka yi mini, amma ni kam ba zan taɓa ka ba.

  14. Kamar yadda karin maganan nan na dā ya ce, ‘Daga cikin masu mugunta, mugunta ke fitowa,’ hannuna dai ba zai taɓa ka ba.

  15. “Wane ne sarkin Isra’ila, ka fito kake bi? Wa kake kora? Kana bin mataccen kare ko kuɗin cizo?

  16. Ubangiji yă zama alƙali, yă yi shari’a tsakanina da kai, bari Ubangiji yă duba, yă tsaya mini, yă nuna ba ni da laifi.”

  17. Zifawa suka je wurin Shawulu a Gibeya suka ce, “Ashe, ba Dawuda ne ya ɓuya a tudun Hakila da yake fuskantar Yeshimon ba?”

  18. Sai Shawulu ya tashi ya gangara zuwa Jejin Zif, tare da zaɓaɓɓun mutane dubu uku na Isra’ila. Suka fita neman Dawuda a can.

  19. Shawulu ya yi sansani a bakin hanyar zuwa tudun Hakila mai fuskantar Yeshimon. Amma Dawuda yana zaune a jeji. Sa’ad da ya ga Shawulu ya biyo shi har zuwa can,

  20. sai ya aiki ’yan leƙen asiri su tabbata lalle Shawulu ya iso can.

  21. Sai Dawuda ya kintsa ya tafi inda Shawulu ya yi sansani. Ya ga inda Shawulu da Abner ɗan Ner shugaban ƙungiyar soja suka kwanta. Shawulu yana kwance a cikin sansani tare da sojoji kewaye da shi.

  22. Sai Dawuda ya ce wa Ahimelek mutumin Hitti da Abishai ɗan Zeruhiya ɗan’uwan Yowab, “Wa zai gangara tare da ni zuwa sansanin Shawulu?” Sai Abishai ya ce, “Zan tafi tare da kai.”

  23. Saboda haka Dawuda da Abishai suka gangara zuwa wurin rundunar da dare, sai ga Shawulu kwance yana barci a cikin sansani da māshinsa a kafe a ƙasa kusa da kansa. Abner kuwa tare da sojoji suna kwance kewaye da shi.

  24. Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Allah ya ba da maƙiyinka a hannunka. Bari in kafe shi da ƙasa da māshina, zan soke shi da māshi sau ɗaya tak, ba na bukata in soke shi sau biyu.”

  25. Amma Dawuda ya ce wa Abishai, “Kada ka hallaka shi. Wa zai sa hannu a kan shafaffe na Ubangiji, har yă tsira?