Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Resurrection

194 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Su kuwa suka amsa, suka ce, ‘A’a, wataƙila ba zai ishe mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’

  2. “Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa.

  3. “An jima can, sai ga sauran sun iso. Suka ce, ‘Ranka yă daɗe! Ranka yă daɗe! Ka buɗe mana ƙofa!’

  4. “Amma ya amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, ban san ku ba.’

  5. “Saboda haka sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ko sa’ar ba.

  6. Kaburbura suka bubbuɗe, jikunan tsarkaka da yawa kuwa cikin waɗanda da suka mutu, suka tashi.

  7. Suka firfito daga kaburbura, sa’an nan bayan tashin Yesu daga matattu, suka shiga birni mai tsarki, suka bayyana ga mutane da yawa.

  8. Sa’an nan Sadukiyawa da suke cewa, babu tashin matattu, suka zo masa da tambaya.

  9. Suka ce, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, in ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata babu ’ya’ya, dole mutumin ya auri gwauruwar, yă kuma samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya.

  10. To, an yi waɗansu ’yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu babu ’ya’ya.

  11. Na biyun ya auri gwauruwar, sai shi ma ya mutu, babu ’ya’ya. Haka kuma na ukun.

  12. A gaskiya, ba ko ɗaya daga cikin bakwai ɗin da ya bar ’ya’ya. Daga ƙarshe, macen ta mutu.

  13. To, a tashin matattu, matar wa za tă zama, don duk su bakwai nan sun aure ta?”

  14. Yesu ya ce, “Ashe, ba a cikin kuskure kuke ba saboda rashin sanin Nassi, ko ikon Allah?

  15. Sa’ad da matattu suka tashi, ba za su yi aure ba, ba kuwa za a ba da su ga aure ba. Za su zama kamar yadda mala’iku suke a cikin sama.

  16. Game da tashin matattu kuwa, ashe, ba ku karanta a cikin littafin Musa ba, game da labarin ɗan kurmin nan mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, yadda Allah ya yi magana da shi ya ce, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’?

  17. Shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne. Kun yi mummunan kuskure!”

  18. Ta haka, za ka sami albarka. Ko da yake ba za su iya biyan ka ba, za a biya ka a ranar tashin masu adalci daga matattu.”

  19. Waɗansu Sadukiyawa da suke cewa, ba tashin matattu, suka zo wurin Yesu da tambaya cewa,

  20. “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, ‘In ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata amma ba ’ya’ya, dole mutumin ya aure gwauruwar, ya samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya.’

  21. To, an yi waɗansu ’yan’uwa bakwai. Na fari ya auri wata mace, ya mutu ba ’ya’ya.

  22. Na biyun,

  23. da na ukun suka aure ta. Haka nan dukansu bakwai suka mutu babu ’ya’ya.

  24. A ƙarshe, ita macen ma ta mutu.

  25. Shin, a tashin matattu, matar wa za tă zama? Tun da su bakwan nan, sun aure ta.”