Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Resurrection

194 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. haka mutum zai kwanta ba zai tashi ba; har sai duniya ta shuɗe mutane ba za su farka ba, ba za su tashi daga barcinsu ba.

  2. “Da ma za ka ɓoye ni a cikin kabari ka ɓoye ni har sai fushinka ya wuce! In da za ka keɓe mini lokaci sa’an nan ka tuna da ni!

  3. In mutum ya mutu, ko zai sāke rayuwa? In haka ne zan daure kwanakin da nake shan wahala har su wuce.

  4. Za ka kira zan kuwa amsa maka; za ka yi marmarin abin da hannunka ya halitta.

  5. Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai, kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya.

  6. Kuma bayan an hallaka fatata, duk da haka a cikin jiki zan ga Allah.

  7. Zan gan shi da kaina da idanuna, Ni, ba wani ba ne. Zuciyata ta cika da wannan tunani!

  8. Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki; jikina kuma zai zauna lafiya,

  9. domin ba za ka yashe ni a kabari ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.

  10. Amma ni, cikin adalci zan ga fuskarka; sa’ad da na farka, zan gamsu da ganin kamanninka.

  11. Amma Allah zai ceci raina daga kabari; tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa. Sela

  12. zai haɗiye mutuwa har abada. Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye daga dukan fuskoki; zai kawar da kunyar mutanensa daga dukan duniya. Ubangiji ne ya faɗa.

  13. Amma matattunka za su rayu; jikunansu za su tashi. Ku da kuke zama a ƙura, ku farka ku kuma yi sowa don farin ciki. Raɓarka kamar raɓar safiya ce; duniya za tă haifi matattunta.

  14. Hannun Ubangiji yana a kaina, ya kuma fitar da ni ta wurin Ruhun Ubangiji ya sa ni a tsakiyar kwarin; yana cike da ƙasusuwa.

  15. Ya sa na kai na komo a ciki, na kuma ga ƙasusuwa masu girma da yawa a ƙasar kwarin, ƙasusuwan da suka bushe ƙwarai.

  16. Sai ya tambaye ni cewa, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa za su iya rayu?” Ni kuwa na ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai kaɗai ka sani.”

  17. Sai ya ce mini, “Ka yi wa waɗannan ƙasusuwa annabci ka ce musu, ‘Busassun ƙasusuwa, ku ji maganar Ubangiji!

  18. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce wa waɗannan ƙasusuwa. Zan sa numfashi ya shiga muku, za ku kuwa rayu.

  19. Zan harhaɗa muku jijiyoyi in sa muku tsoka in kuma rufe ku da fata; zan sa numfashi a cikinku, za ku kuwa rayu. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

  20. Saboda haka sai na yi annabci yadda aka umarce ni. Da nake annabcin, sai aka ji motsi, ƙarar girgiza, sai ƙasusuwan suka harhaɗu, ƙashi ya haɗu da ƙashi.

  21. Na duba, sai ga jijiyoyi da nama suka bayyana a kansu fata kuma ta rufe su, amma ba numfashi a cikinsu.

  22. Sa’an nan ya ce mini, “Ka yi annabci wa numfashi; ka yi annabci, ɗan mutum, ka ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ka fito daga kusurwoyi huɗu, ya numfashi, ka kuma numfasa cikin waɗannan matattu, don su rayu.’ ”

  23. Saboda haka na yi annabci yadda aka umarce ni, sai numfashi ya shiga musu; suka rayu suka kuma miƙe tsaye a ƙafafunsu babbar runduna ce ƙwarai.

  24. Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa su ne dukan gidan Isra’ila. Suna cewa, ‘Ƙasusuwanmu sun bushe, sa zuciyarmu duk ya tafi; an share mu ƙaf.’

  25. Saboda haka yi annabci ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ya mutanena, zan buɗe kaburburanku in fitar da ku daga cikinsu; zan mai da ku ƙasar Isra’ila.