Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Precious Stones: Pearl
Ayoyi game da Pearl
Kada ma a ce murjani da duwatsu masu walƙiya; farashin hikima ya fi na lu’ulu’ai.
“Har wa yau dai, mulkin sama yana kama da ɗan kasuwa mai neman lu’ulu’ai masu kyau.
Da ya sami dutse guda mai daraja sosai, sai ya tafi ya sayar da dukan abin da yake da shi ya saye shi.
Ƙofofi goma sha biyun nan lu’ulu’ai goma sha biyu ne, kowace ƙofa an yi ta da lu’ulu’u guda. Babban titin birnin kuwa an yi shi da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi.