Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Precious Stones: Adorning the breastplate of judgment

9 ayoyi · 52 fannoni

Ayoyi game da Adorning the breastplate of judgment

  1. Sa’an nan ka yi jeri huɗu na duwatsu masu daraja a kansa. A jeri na fari, a sa yakutu, da tofaz, da zumurrudu.

  2. A jeri na biyu, a sa turkuwoyis, da saffaya, da emeral.

  3. A jeri na uku, a sa yakin, da idon mage da ametis.

  4. A jeri na huɗu, a sa kirisolit, da onis, da yasfa. Ka sa su a tsaiko na zinariya.

  5. Sa’an nan suka sa jeri huɗu na duwatsu masu daraja a bisansa. A jeri na farko akwai yakutu, da tofaz, da zumurrudu;

  6. a jeri na biyu akwai turkuwoyis, da saffaya, da daimon;

  7. a jeri na uku akwai yakinta, da idon mage, da ametis;

  8. a jeri na huɗu akwai beril, da onis, da yasfa. Aka sa su cikin tsaiko na zinariya.

  9. Aka zāna duwatsu goma sha biyu, ɗaya don kowane sunan ’ya’yan Isra’ila goma sha biyu, kamar yadda akan yi hatimi.