Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Midianites

83 ayoyi · 28 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. To, dukan Midiyawa, Amalekawa da sauran mutanen gabashi suka haɗa ƙarfi suka ƙetare Urdun suka kafa sansani a Kwarin Yezireyel.

  2. Ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho da tulu da acibalbal a ciki.

  3. Ya ce musu, “Ku dube ni, ku bi abin da na yi. Sa’ad da na kai sansanin, ku yi daidai abin da na yi.

  4. Sa’ad da ni da dukan waɗanda suke tare da ni muka busa ƙahoninmu, to, ko’ina a kewayen sansanin sai ku busa naku ku kuma yi ihu, ku ce, ‘Don Ubangiji da kuma domin Gideyon.’ ”

  5. Gideyon da mutum ɗari da suke tare da shi suka kai sansanin da tsakar dare bayan an sauya matsara. Suka busa ƙahoninsu, suka farfashe tulunansu da suke hannuwansu.

  6. Ƙungiyoyi uku ɗin nan suka busa ƙahonin, suka fasa tuluna. Suka ɗauki acibalbal a hannuwansu na hagu da ƙahonin busawa a hannuwansu na dama, sai suka yi ihu, “Takobi don Ubangiji da kuma don Gideyon!”

  7. Yayinda kowannensu ya tsaya a inda yake kewaye da sansanin, dukan Midiyawa suka fito da gudu, suna kuka yayinda suke gudu.

  8. Sa’ad da aka busa ƙahonin nan ɗari uku sai Ubangiji ya sa Midiyawa suka yi ta saran juna. Mayaƙan suka gudu zuwa Bet-Shitta wajen Zerera har zuwa yankin Abel-Mehola kusa da Tabbat.

  9. Gideyon ya aiki manzanni zuwa dukan ƙasar tudu ta Efraim cewa, “Ku gangaro ku yaƙi Midiyawa ku ƙwace ruwan Urdun gaba da su har zuwa Bet-Bara.” Saboda haka aka kira dukan mutanen Efraim suka ƙwace ruwan Urdun har zuwa Bet-Bara.

  10. Suka kuma kama shugabannin biyu na Midiyawa, Oreb da Zeyib suka kashe Oreb a dutsen Oreb, Zeyib kuma a wurin matsin ruwa inabin Zeyib. Suka fatattaki Midiyawa suka kawo kawunan Oreb da Zeba wurin Gideyon, wanda yake kusa da Urdun.

  11. Ya ce wa mutanen Sukkot, “Ku ba wa mutanena burodi; sun gaji, har yanzu ina fafarar Zeba da Zalmunna, sarakunan Midiyawa.”

  12. To, Zeba da Zalmunna suna a Karkor da mayaƙa wajen dubu goma sha biyar, abin da ya rage ke nan na mayaƙan gabashi; mayaƙa masu takobi dubu ɗari da ashirin ne suka mutu.

  13. Gideyon ya haura ta hanyar makiyaya, gabas da Noba, da kuma Yogbeha, ya fāɗa wa mayaƙan ta yadda ba su zata ba.

  14. Zeba da Zalmunna, sarakunan biyu na Midiyawa suka tsere, amma ya bi su ya kama, ya fatattaki dukan mayaƙansu.

  15. Zeba da Zalmunna suka ce masa, “Zo, ka yi da kanka. ‘Yadda mutum yake haka ƙarfinsa.’ ” Ta haka Gideyon ya matso gaba ya kashe su, ya ɗauki kayan ado daga wuyar raƙumansu.

  16. Kuma ya ce, “Ina da roƙo guda ɗaya, cewa kowannenku ya ba ni ’yan kunne daga rabon ganima.” (Al’adar mutanen Ishmayel ce su sa ’yan kunnen zinariya.)

  17. ’Ya’yan Ketura maza, ƙwarƙwarar Ibrahim su ne, Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa. ’Ya’yan Yokshan maza su ne, Sheba da Dedan.

  18. ’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida da Elda’a. Dukan waɗannan su ne zuriyar Ketura.

  19. Sa’ad da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a cikin ƙasar Mowab, ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Awit.

  20. Ka yi musu abin da ka yi wa Midiyan, yadda ka yi wa Sisera da Yabin a kogin Kishon,

  21. waɗanda suka hallaka a En Dor suka zama kamar juji a ƙasa.

  22. Ka mai da manyansu kamar Oreb da Zeyib, dukan sarakunansu kamar Zeba da Zalmunna,

  23. Gama kamar yadda yake a kwanakin da aka ci Midiyan da yaƙi, kuka ji tsoro nauyin da ya nawaita musu, sandar da yake a kafaɗunsu, sandar masu zaluncinsu.

  24. Ubangiji Maɗaukaki zai bulale su da tsumagiya, kamar sa’ad da ya bugi Midiyan a dutsen Oreb; zai kuma ɗaga sandarsa a bisa ruwaye, yadda ya yi a Masar.

  25. Manyan ayarin raƙuma za su cika ƙasar, ƙananan raƙuma ke nan daga Midiyan da Efa. Daga Sheba kuma duka za su zo, suna ɗauke da zinariya da turare suna shelar yabon Ubangiji.