Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Egypt

328 ayoyi · 105 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Shanun nan ramammu, munana, da suka zo daga baya, shekaru bakwai ne, haka ma kawuna dawan nan shanyayyu da iskar gabas ta yanƙwane. Shekaru ne bakwai na yunwa.

  2. “Haka yake kamar yadda na faɗa wa Fir’auna cewa Allah ya nuna wa Fir’auna abin da yake shirin yi.

  3. Shekaru bakwai na yalwar abinci suna zuwa a dukan ƙasar Masar,

  4. amma shekaru bakwai na yunwa za su biyo bayansu. Tsananin yunwar za tă sa a manta da dukan isashen abincin da aka samu a ƙasar Masar, yunwa kuwa za tă rufe dukan ƙasar.

  5. Ba za a tuna da isashen abincin da aka samu a ƙasar ba, domin yunwar da za tă biyo baya za tă zama da tsanani ƙwarai.

  6. Dalilin da aka ba wa Fir’auna mafarkan nan kashi biyu kuwa shi ne cewa Allah ya riga ya ƙaddara al’amarin. Allah zai aikata shi, ba da daɗewa ba.

  7. “Yanzu fa, bari Fir’auna yă nemi mutum mai basira da kuma hikima, yă sa shi yă shugabanci ƙasar Masar.

  8. Bari Fir’auna yă naɗa komishinoni a kan ƙasar don su karɓi kashi ɗaya bisa biyar na girbin Masar a lokacin shekaru bakwai na yalwar abinci.

  9. Ya kamata su tara dukan abincin waɗannan shekaru masu kyau da suke zuwa, su yi ajiyar hatsin a ƙarƙashin ikon Fir’auna, don a ajiye a birane don abinci.

  10. Ya kamata a adana abincin nan don ƙasar, kāriya shekaru bakwai na yunwa, domin a yi amfani da shi a lokacin shekarun yunwan da za su zo wa Masar, saboda kada ƙasar ta lalace da yunwa.”

  11. Saboda haka Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Ga shi na sa ka zama shugaban dukan ƙasar Masar.”

  12. Sa’an nan Fir’auna ya zare zoben sarauta daga yatsarsa, ya sa shi a yatsan Yusuf. Ya sanya masa rigar lallausan lilin, ya kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa.

  13. Ya sa shi ya hau keken yaƙi a matsayi mai binsa na biyu, mutane kuwa suka yi shela a gabansa suna cewa, “A ba da hanya!” Ta haka ya sa shi shugaba a kan dukan ƙasar Masar.

  14. Sa’an nan Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Ni ne Fir’auna, amma in ba tare da umarninka ba, ba wanda zai ɗaga hannu ko ƙafa a cikin dukan Masar.”

  15. Yusuf yana zuwa shekara talatin sa’ad da ya shiga hidimar Fir’auna sarkin Masar. Yusuf kuwa ya fita daga gaban Fir’auna, ya zaga ko’ina a Masar.

  16. A shekaru bakwai na yalwa, ƙasar ta ba da amfani mai yawa.

  17. Yusuf ya tattara dukan abincin da aka samu a waɗannan shekaru bakwai na yalwa a Masar, ya kuma yi ajiyarsu a cikin birane. A kowane birni, ya sa abincin da aka nome a kewayensa.

  18. Sai Yusuf ya tara hatsi da yawan gaske, kamar yashi a bakin teku, har sai da ya kāsa iya auna shi, gama ba a iya aunawa.

  19. Kafin shekarun yunwa su zo, Asenat ’yar Fotifera, firist na On, ta haifa wa Yusuf ’ya’ya maza biyu.

  20. Yusuf ya ba wa ɗansa na fari suna Manasse ya ce, “Gama Allah ya sa na mance dukan wahalata da dukan gidan mahaifina.”

  21. Ya ba wa ɗansa na biyu suna Efraim ya ce, “Gama Allah ya wadata ni cikin wahalata.”

  22. Shekaru bakwai na yalwa a Masar suka zo ga ƙarshe,

  23. sai shekaru bakwai na yunwa suka soma shigowa, kamar yadda Yusuf ya faɗa. Aka yi yunwa ko’ina amma ban da ƙasar Masar. Don akwai abinci.

  24. Sa’ad da dukan Masar ta fara jin yunwa, sai mutane suka yi wa Fir’auna kuka don abinci. Sai Fir’auna ya ce wa dukan Masarawa, “Ku tafi wurin Yusuf, ku kuma yi abin da ya faɗa muku.”

  25. Sa’ad da yunwa ta bazu a dukan ƙasar, sai Yusuf ya buɗe gidajen ajiya, ya kuma sayar da hatsi ga Masarawa, gama yunwa ta yi tsanani a dukan Masar.