Thebes
An kuma san shi da: No
25.7000, 32.6300 Duba a Google Maps
Ayoyin da suka ambaci Thebes
Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Ina gab da kawo hukunci a kan allahn Amon na Tebes, a kan Fir’auna, a kan Masar da allolinta da sarakunanta, da kuma a kan waɗanda suka dogara ga Fir’auna.
Zan lalace Masar ta Bisa in ƙuna wuta wa Zowan in zartar da hukunci a kan Tebes.
Zan kwarara hasalata a kan Felusiyum, kagarar Masar, in kuma datse mutanen Tebes.
Zan ƙuna wuta wa Masar; Felusiyum za tă sha azaba mai zafi. Za a tayar wa Tebes da hankali; Memfis za tă riƙa kasance cikin ɓacin rai.
Kin fi Tebes ne da take a bakin Nilu, da ruwa yake kewaye da ita? Rafi shi ne kāriyarta, ruwanta kuma katanga.