Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Egypt: Joseph made governor

4 ayoyi · 105 fannoni

Ayoyi game da Joseph made governor

  1. Saboda haka Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Ga shi na sa ka zama shugaban dukan ƙasar Masar.”

  2. Sa’an nan Fir’auna ya zare zoben sarauta daga yatsarsa, ya sa shi a yatsan Yusuf. Ya sanya masa rigar lallausan lilin, ya kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa.

  3. Ya sa shi ya hau keken yaƙi a matsayi mai binsa na biyu, mutane kuwa suka yi shela a gabansa suna cewa, “A ba da hanya!” Ta haka ya sa shi shugaba a kan dukan ƙasar Masar.

  4. Sa’an nan Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Ni ne Fir’auna, amma in ba tare da umarninka ba, ba wanda zai ɗaga hannu ko ƙafa a cikin dukan Masar.”